Mutum ɗaya ya mutu a rikicin manoma da makiyaya a Jigawa

Mazauna yankin sun ce rikicin ya afku ne a ranar Juma’a a Unguwar Gululu, inda manoman suka zargi makiyayan da yin sata a cikin shaguna.

Mutum ɗaya ya mutu a rikicin manoma da makiyaya a Jigawa

An tabbatar da mutuwar mutum ɗaya tare da jikkata wasu huɗu a wani rikici da ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya a Ƙaramar hukumar Miga ta Jihar Jigawa.

Mazauna yankin sun ce rikicin ya afku ne a ranar Juma’a a Unguwar Gululu, inda manoman suka zargi makiyayan da yin sata a cikin shaguna a daren Juma’a.

Dakacin garin Gululu, Muhammad Sarkin-Dori, ya shaida wa Aminiya cewa wasu mazauna ƙauyen Gululu ne suka bi sawun ɓarayin zuwa wata Unguwar makiyaya domin neman kayan da suka sace.

“Mun tashi da safiyar yau Juma’a ne sai muka ga wani kantin sayar da kayayyaki an fasa wanda da ake zargin ɓarayi ne suka ɓalle, inda wasu mazauna garin suka yanke shawarar bin sawun ɓarayin wanda ya kai su ga yankin Fulani a wurin rikicin ya ɓarke.

“Makiyayan sun tunkari mutanen da harbin baka da kibiya bayan sun gansu a matsugunansu, har yanzu ba a bayyana ko an ƙwato kayan da aka sace a wurin ba, amma mun roƙi a kwantar da hankula kuma mun kai rahoto ga jami’an tsaro.” Cewar Basaraken.

Sarkin-Dori ya ce, kimanin mutane biyar ne aka kai su asibitin koyarwa na Aminu Kano bayan tun farko an fara kai su a babban asibitin Jahun da ke jihar.

Ya ce mutum ɗaya mai suna Dauda Kafinta, wanda aka bayyana ɓacewarsa a yayin fafatawar daga baya an samu gawarsa da raunukan baka da kibiya.