Mutum 10 sun mutu a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri

Haɗarin ya auku ne yayin da wata motar dakon kaya maƙare da siminti ta yi ƙundumbala ta faɗa wani rami.

Mutum 10 sun mutu a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri

An tabbatar da mutuwar mutum 10 a sakamakon wani haɗari da ya auku a  babbar hanyar Damaturu zuwa Maiduguri a Jihar Yobe.

Haɗarin wanda ya jikkata mutum uku ya auku ne shingen binciken ababen hawa da jami’an tsaro suka kafa a daidai garin Warsala.

Bayanai sun ce haɗarin ya auku ne yayin da wata motar dakon kaya maƙare da siminti ta yi ƙundumbala ta faɗa wani rami.

Wata majiya ta ce fasinjoji 13 ne a cikin motar wanda 10 daga ciki suka mutu nan take yayin da ragowar ukun suka jikkata..

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Yobe, SP Dungus Abdulkarim, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce an kai waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Ƙwararru da ke Damaturu domin ba su kulawar gaggawa.

A cewarsa, binciken da aka gudanar ya gano cewa tsinkewar birki ne ya haddasa aukuwar haɗarin wanda kuma ya haɗa da wata ƙaramar mota ƙirar Sharon.

Mutum 10 sun mutu a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri

Babu hannun Naira Marley a mutuwar Mohbad — Kotu

Tattalin arzikin Nijeriya ya haɓaka da kashi 3.84 — NBS

An naɗa Obasanjo mai shiga tsakani a rikicin Kongo