Mutum 15 sun mutu a sabon harin Kudancin Kaduna- ‘Yan sanda

Hukumar ‘yan sandan jihar Kaduna sun tabbatar da rasuwar mutum 15 da raunata 24  yayin da wasu ‘yan bindiga suka kai wani sabon hari  a garin Ungwan Pah II da ke unguwar Gwandara a  karamar hukumar Jama’a jihar Kaduna. Jami’in hulda da jama’a na hukumar ‘yan sandan jihar DSP Yakubu Sabo ya bayyana wa majiyarmu […]

Mutum 15 sun mutu a sabon harin Kudancin Kaduna- ‘Yan sanda

Hukumar ‘yan sandan jihar Kaduna sun tabbatar da rasuwar mutum 15 da raunata 24  yayin da wasu ‘yan bindiga suka kai wani sabon hari  a garin Ungwan Pah II da ke unguwar Gwandara a  karamar hukumar Jama’a jihar Kaduna.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar ‘yan sandan jihar DSP Yakubu Sabo ya bayyana wa majiyarmu hakan.

Sabo ya ce, a yanzu haka Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ahmad Abdulrahman ya bayar da umarnin a binciko wadanda suke da alhakin kai harin a yankunan.