Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja

Rahotanni sun nuna cewar lamarin ya auku ne da safiyar ranar Asabar.

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja

Aƙalla mutum 10 ne sun rasa rayukansu, wasu kuma da dama sun jikkata yayin wani turmutsutsi da ya faru a Cocin Holy Trinity Catholic Church da ke Maitama, Abuja, a ranar Asabar.

Rahotanni, sun bayyana cewa turmutsutsin ya faru ne lokacin da ake raba tallafin abinci a cocin.

Rundunar  yan sandan Abuja, ta tabbatar da aukuwar lamarin tare da adadin waɗanda suka mutu.

Kakakin rundunar, SP Josephine Adeh, ta ce yara huɗu na daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu.

Hakazalika, ta ce mutum takwas sun samu raunuka daban-daban.

“Mutum huɗu daga cikin waɗanda suka jikkata an sallame su bayan samun kulawa a asibiti,” in ji SP Adeh.

Bayanai, sun nuna cewa an shirya rabon tallafin ne don taimaka wa mabuƙata yayin shirin bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara.

Wasu da suka shaida faruwar lamarin, sun ce turmutsutsin ya faru ne da misalin karfe 7 na safiyar ranar Asabar.

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja

Tirela murƙushe ’yan sanda 3 har lahira