Mutum 10 sun rasu, 12 sun ji rauni a hatsarin mota a Jigawa

Motocin biyu sun yi karo da juna sakamakon gudun wuce kima.

Mutum 10 sun rasu, 12 sun ji rauni a hatsarin mota a Jigawa

Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) ta tabbatar da mutuwar mutum 10, yayin da wasu 12 suka samu raunuka a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a hanyar Ringim zuwa Dutse da ke Karamar Hukumar Ringim ta Jihar Jigawa.

Kakakin hukumar, Ibrahim Yahaya ne ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) faruwar lamarin a Dutse.

Yahaya ya ce hatsarin ya faru ne tsakanin wata mota kirar Volkswagen Golf da wata bas kirar Toyota a kauyen Gidan Garke da misalin karfe 12:30 na ranar Alhamis.

Ya bayyana cewa hatsarin ya auku ne lokacin da motocin biyu ke dauke da fasinjoji 22, suka yi karo da juna sakamakon gudun wuce kima.

Kakakin ya ce jami’an hukumar sun kai wadanda abin ya shafa zuwa babban Asibitin Ringim.

A cewarsa, jami’an ba su iya tantance lambobin motocin biyu ba saboda sun kone kurmus.

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda

An saki matar Ekweremadu daga gidan yari a Birtaniya, ta dawo Najeriya

Trump ya bayar da umarnin kamen ’yan gudun hijira a Amurka