Mutum 10 sun rasu bayan cin abinci a wurin daurin aure
Mutum goma sun rasu a shekaranjiya Laraba bayan sun ci abinci a wurin daurin aure a Unguwar dandagoro da ke karamar Hukumar batagarawa a kusa da birnin Katsina a Jihar Katsina. Labarin da shirin Barkete Family da wani gidan rediyo a Abuja ke gabatarwa ya ce mutane da dama da suka ci abincin ko suka […]
Mutum goma sun rasu a shekaranjiya Laraba bayan sun ci abinci a wurin daurin aure a Unguwar dandagoro da ke karamar Hukumar batagarawa a kusa da birnin Katsina a Jihar Katsina.
Labarin da shirin Barkete Family da wani gidan rediyo a Abuja ke gabatarwa ya ce mutane da dama da suka ci abincin ko suka sha kayan zaki da aka tanada a wurin daurin aure an garzaya da su Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya bayan da suka yi kukan ciwon ciki tare da gudawa a lokacin.
Wata majiya a inda asibitin yake a kan Titin Murtala Muhammad da ke birnin Katsina ta ce a tsakanin abinci ko ruwa da kayan zakin da aka ba mahalarta daurin auren suka ci ko suka sha a wurin bikin ne daya yake da guba. Kuma an gano akwai wasu da suka halarci daurin auren da aka kwantar a wasu asibitoci a sassan jihar.
Lamarin ya jawo an soke tare da dage daurin aure biyu da aka shirya yi a cikin makon nan, saboda kasancewar wadanda suka samu kansu a cikin wannan hali kodai su ne za su angwance ko su za su amarce.
Idan za a tuna ga al’ada akan yi ta bukukuwan aure a nan Arewa a duk lokacin da azumin Ramadan ya kusato, kuma ana sa ran fara azumin watan Ramadan na bana a ranar 17 ko 18 ga wannan wata na Yuni.