Mutum 10 sun rasu sakamakon bullar wata cuta a Yawuri

Sama da mutum goma ne suka rasu sakamakon bullar wata cuta a Kasuwar ’Yan Albasa da ke bakin Kogin Yawuri da ke Jihar Kebbi.Wani mazaunin yankin mai suna Is’haka Sani da ke zuwa kasuwar, ya shaida wa wakilinmu cewa ana zargin barkewar cutar na da nasaba da albasar da ake zubarwa tana rubewa da kuma […]

Mutum 10 sun rasu sakamakon bullar wata cuta a Yawuri
Mutum 10 sun rasu sakamakon bullar wata cuta a Yawuri

Sama da mutum goma ne suka rasu sakamakon bullar wata cuta a Kasuwar ’Yan Albasa da ke bakin Kogin Yawuri da ke Jihar Kebbi.
Wani mazaunin yankin mai suna Is’haka Sani da ke zuwa kasuwar, ya shaida wa wakilinmu cewa ana zargin barkewar cutar na da nasaba da albasar da ake zubarwa tana rubewa da kuma fistari da bayan gida da ake yi a kusa da kogin wanda mutane suke shiga suna wanka a ciki. Ya ce ana fara gane alamun mutum ya kamu da cuta ta hanyar fara jin ciwon kai.
Da wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin Babban Sakatare a Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kebbi, Alhaji Abubakar Kande game da bullar cutar, amma har sau biyu yana zuwa ofishinsa bai same shi ba, kuma ya kira shi a waya bai dauka ba, sanna bai maida masa da sakon tes da ya aika masa ba.
Sai dai wani darakta a ma’aikatar da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da bullar cutar, inda ya ce ciwon sankarau ne da zazzabin maleriya.
Ya kara da cewa gwamnatin jihar ta dauki kwararan matakai domin shawo kan wannan ciwo inda ta sayo magunguna domin rarrabawa ga masu zuwa kasuwar ta ’yan albasa da wadanda suke kusa da wurin domin rigakafin wannan ciwo.
Ya ce tun lokacin da ma’aikatansu suka isa Yawuri ba su sake jin labarin wani ya sake kamuwa da cutar ba. Sai ya jawo hankalin jama’a su kasance masu tsaftace muhalli a koyaushe kuma su guji shan ruwa marar kyau, sannan a rika barin tagogi a bude idan za a kwanta barci don kauce wa kamuwa da sankarau.