Mutum 10,000 na neman a dauke su aikin Amotekun

Akalla mutum 10,000 ke neman a dauke su aikin tsaro na Amotekun a yankin Kudu maso-Yammacin Najeriya. Kwamandan Rundunar Amotekun, Adetunji Adeleye, ya ce ana ci gaba da aikin tantance sama da mutum 10,000 din ne kafin a horas da wadanda suka yi nasara daga cikinsu. Ya bayyana haka ne a yayin da yake cewa […]

Mutum 10,000 na neman a dauke su aikin Amotekun

Amotekun

Akalla mutum 10,000 ke neman a dauke su aikin tsaro na Amotekun a yankin Kudu maso-Yammacin Najeriya.

Kwamandan Rundunar Amotekun, Adetunji Adeleye, ya ce ana ci gaba da aikin tantance sama da mutum 10,000 din ne kafin a horas da wadanda suka yi nasara daga cikinsu.

Ya bayyana haka ne a yayin da yake cewa jami’an rundunar sun yi nasarar kama shanu 42 da suka barnata wasu gonaki a yankin.

Jihohin Kudu maso-Yammacin Najeriya sun kafa runduanr ne domin aiki tare da sauran hukumomin tsaro wajen magance rikicin manoma da makiya da sauran matsalolin tsaro a yankin.

A cewar Adeleye, masu shanun, dauke da makamai sun nemi su far musu a sadda suka kai dauki bayan yawaitar koke-koke daga masu gonakin.

Ya ce da jami’an tsaro suka fi karfin makiyayan, sai suka tsere suka bar dabbobin da aka yi nasarar kamawa.

Da yake gargadin makiyaya da su guji shiga gonaki, Adeleye ya ce masu dabbobin za su biya barnar da shanun suka yi a gonakin sannan a gurfanar da su a kotu.

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50