Mutum 100,000 sun mutu a rikicin da ya dabaibaye Myanmar bayan juyin mulkin 2021

Juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Fabrairun 2021 ya kifar da gwamnatin farar hula ta Aung San Suu Kyi.

Mutum 100,000 sun mutu a rikicin da ya dabaibaye Myanmar bayan juyin mulkin 2021

Mutum sama da 100,000 ne suka rasa rayukansu a rikicin da ya dabaibaye Myanmar tun bayan juyin mulkin soji da aka yi a shekarar 2021, a cewar sabbin alƙaluman ƙungiyar sa ido kan rikice-rikice ta ACLED.

Juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Fabrairun 2021 ya kifar da gwamnatin farar hula ta Aung San Suu Kyi, inda aka tsare tsohuwar shugabar ƙasar tare da kawo ƙarshen gwajin tsarin mulkin dimokuraɗiyyar da ƙasar ta fara.

Bayan murƙushe zanga-zangar adawa da juyin mulkin, masu rajin dimokuraɗiyya sun koma karkara inda suka kafa ƙungiyoyin mayaƙa tare da haɗa kai da ƙungiyoyin ƙabilu masu ɗauke da makamai da suka daɗe suna yaƙi da gwamnati.

Alƙaluman ACLED sun nuna cewa ya zuwa yanzu an tabbatar da mutuwar mutane 100,114 masu alaƙa da rikicin, duk da cewa babu alƙaluman da aka fitar hukumance, kuma masana na kallon rikicin a matsayin mafi muni da ke ci gaba da gudana a nahiyar Asiya.

Wata mata mai suna Thein Aye Nu, wadda mijinta ya mutu sakamakon harin sama a jihar Rakhine a watan da ya gabata, ta ce ba ta da kalmomin bayyana irin baƙin cikin da take ciki.

Ta ce, “Raɗaɗin da nake ji ba ya gushewa. Ina cike da baƙin ciki da fushi, amma ban ma san wa zan ɗora wa laifi ba.”

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce sama da mutum miliyan 3.7 sun rasa matsugunansu a cikin ƙasar, yayin da fiye da mutum ɗaya cikin biyar ke fama da matsanancin ƙarancin abinci sakamakon rikicin da ya jefa ƙasar cikin talauci.

Rahoton ya kuma nuna cewa rikicin ya bazu zuwa kusan duk sassan ƙasar, inda hare-haren sama, artabu tsakanin sojoji da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai, da kashe-kashe ke ci gaba da aukuwa.

ACLED ta ce rikicin ya haɗa da ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai sama da 1,200, lamarin da ya sa ake kallonsa a matsayin rikicin da ya fi kowane ɓangare tarwatsewa a duniya.

Masana sun ce bayan nasarorin da ƙungiyoyin ’yan tawaye suka samu a ƙarshen shekarar 2023, sojojin Myanmar sun fara sake samun rinjaye, musamman bayan goyon bayan da suka samu daga China da kuma yarjejeniyoyin tsagaita wuta da wasu manyan ƙungiyoyin ƙabilu suka ƙulla.

Rikicin ya kuma haddasa kwararar ’yan gudun hijira zuwa ƙasashe maƙwabta kamar Thailand da Bangladesh, tare da ƙara ta’azzara safarar miyagun ƙwayoyi da cibiyoyin damfara ta intanet a yankunan kan iyaka.