Mutum 11 ne suka mutu a harin Cocin Anambara-’Yansanda
Rundunar ’yan sandan jihar Anambara ta ce mutum 11 ne suka mutu sannan 18 suka jikkata a harin da wasu ’yan bindiga suka kai Cocin Saint Philips a kauyen Ozubulu da ke karamar hukuamr Ekwusigo da ke cikin jihar Anambara a jiya Lahadi. Kwamishinan ’Yansandan jihar, Mista Garba Umar shi ne ya bada tabbacin yayin […]
Rundunar ’yan sandan jihar Anambara ta ce mutum 11 ne suka mutu sannan 18 suka jikkata a harin da wasu ’yan bindiga suka kai Cocin Saint Philips a kauyen Ozubulu da ke karamar hukuamr Ekwusigo da ke cikin jihar Anambara a jiya Lahadi.
Kwamishinan ’Yansandan jihar, Mista Garba Umar shi ne ya bada tabbacin yayin da yake zantawa da wakilin sashen Hausa na gidan rediyon BBC, a yau Litinin.
Umar ya ce tuni rundunar ta baza komarta don kamo wadanda suka aikata kisan gillar tare da gurfanar da su a gaba kotu.
“Kamar yadda muka kirga mutane 11 sun rasa rayukansu, sannan mutane 18 suna asibiti ana kula da su”. Inji shi
Ya bada tabbacin cewa rundunar ta dukufa wajen ganin ta kamo wadanda suka aikata danyen aikin tare da gurfanar da su a gaban kotu.
Kwamishinan wanda ya ce rikicin ba na addini ko kabilanci ba ne ya dage a kan cewa rikici ne tsakanin ’yan asalin garin da ke zaune a Kasar Afirka Ta Kudu.
’Yan bindiga sun yi wa cocin Katolika ta Saint Philips a kauyen Ozubulu da ke Karamar Hukumar Ekwusigo a cikin jihar Anambara inda suka bude wuta kan masu bauta har suka kashe da dama daga cikinsu.
Wani wanda lamarin ya auku a kan idonsa ya fada wa Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya cewa a ranar Lahadi ’yan bindigar suka shiga cocin lokacin da masu bauta suke ibada da misalin karfe biyar da minti 45 na dare suka harbe wani mutum.
Ya bayyana cewa daga bisani sai ’yan bindigar suka yi harbin kan mai-uwa-da-wabi a kan membobin cocin inda suka kashe mutane masu yawa.