Mutum 11 sun mutu a haɗarin mota a Kaduna

Dukkan mutanen 11 da suka rasu a haɗarin ya shafa na cikin motar Golf

Mutum 11 sun mutu a haɗarin mota a Kaduna

Mummunan haɗarin mota da ya rutsa da wata tirela da wata mota ƙirar Golf, ya yi sanadin mutuwar fasinjoji 11 a hanyar Kaduna zuwa Zariya.

An samu rahoton cewa lamarin ya faru ne a yankin Gwargwaje da ke a Zariya da misalin ƙarfe 5:50 na safiyar ranar Juma’a.

Bayanai sun ce dukkan mutanen 11 da suka rasu a haɗarin ya shafa na cikin motar Golf mai lamba FST 134FƊ.

Kwamandan hukumar kiyaye haɗɗura ta ƙasa reshen Jihar Kaduna, Kabir Nadabo, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar, yana mai cewa fasinjoji huɗu sun samu raunuka.

Nadabo ya bayyana cewa, jami’an ‘yan sanda daga sashin Gwargwaje sun gudanar da aikin ceton sannan daga bisani suka sanar da su.

“Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa, motar Golf mai ɗauke da mutum 11 (duk maza) ta shiga hannun da ba nata ba kuma ba tare da fitilun mota, inda ta yi karo da wata tirela da ke tafe da mutane huɗu a cikinta.

“Mummunan haɗarin ya yi sanadiyar mutuwar mutane 11 da ke cikin motar Golf, yayin da mutane huɗu da ke cikin tirelar suka samu raunuka.

“Bayan kammala aikin ceto an mika duk waɗanda lamarin ya shafa zuwa Asibitin Koyarwa na Jamiar Ahmadu Bello da ke Shika,” in ji shi.