Mutum 11 sun rasu a rikicin manoma da makiyaya a Katsina

Rahotanni na bayyana cewa, mutum 11 sun rasu sanadiyyar rikicin da ya faru tsakanin manoma da makiyaya a kauyen Gora na Karamar Hukumar Safana da ke jihar Katsina. Rikicin ya faru ne a daren jiya lokacin da wani manomi ke aiki a gonarsa, wani da ake zargin makiyayi ne rikici ya kaure tsakaninsu har ya […]

Mutum 11 sun rasu a rikicin manoma da makiyaya a Katsina

Rahotanni na bayyana cewa, mutum 11 sun rasu sanadiyyar rikicin da ya faru tsakanin manoma da makiyaya a kauyen Gora na Karamar Hukumar Safana da ke jihar Katsina.

Rikicin ya faru ne a daren jiya lokacin da wani manomi ke aiki a gonarsa, wani da ake zargin makiyayi ne rikici ya kaure tsakaninsu har ya kashe manomin.

Kakakin Hukumar ‘yan sandan jihar SP Gambo Isah, ya ce a yanzu haka an tura jami’an tsaro yankin don tabbatar da zaman lafiya a yankin.