Mutum 11 sun rasu, an ƙone gidaje a rikicin Hausawa da Fulani a Jigawa
Mazauna yankin sun yi kira da gwamnati ta kawo musu ɗauki domin samun zaman lafiya.
Mutum 11 sun rasa rayukansu, yayin da gidaje 31 suka ƙone ƙurmus a rikicin ƙabilanci tsakanin Hausawa da Fulani a ƙauyen Gululu, da ke ƙananan hukumomin Jahun da Miga na Jihar Jigawa.
Wani dattijon Fulatani da ya rasa ’ya’ya biyar, Suleiman Abubakar Jahun, ya bayyana rikicin ya faru.
- ’Yan bindiga sun sake sace mutum 46 a Zamfara
- Yadda na taso daga almajiranci na zama shugaban NNPCL – Kyari
“Na isa wajen da abin ya faru sai kawai na tarar ana kashe-kashe.
“Yarana ba su da hannun a rikicin, amma su ma sun rasa rayukansu. Yanzu jikoki 18 ne suka rage min da zan ci gaba da kula da su.”
Wani mutum da rikicin ya shafa, Amadu Garba Jahun, wanda ya rasa ɗansa, ya yi kira da a samar da zaman lafiya.
“Ba za mu yi ramuwar gayya ba. Muna son gwamnati ta ɗauki mataki kuma ta yi mana adalci,” in ji shi.
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA), ta bayar da tallafin abinci da kuɗi ga waɗanda abin ya shafa.
SEMA, ta ce rikicin ya samo asali ne daga satar kaya da ya rikiɗe zuwa rikici.
Hukumomi na ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya, inda ‘yan sanda suka sha alwashin kama masu hannu a rikicin tare da yin kira ga al’umma su zauna lafiya.