Mutum 12 sun rasu, 5 sun jikkata a hatsarin mota a Kano
Kwamandan hukumar ya gargaɗi direbobi kan kiyaye dokokin hanya.
Mutum 12 sun rasu yayin da wasu biyar suka jikkata a wani hatsarin mota da ya auku a ƙauyen Samawa, da ke Ƙaramar Hukumar Garun Malam a Jihar Kano.
Hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:40 na daren ranar Juma’a a kan titin Zariya zuw Kano.
Tirela ƙirar DAF mai lambar KMC 931 ZE, wadda ke ɗauke da kaya da fasinjoji ta yi hatsarin.
Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC) reshen Kano, ta ce bincike ya nuna cewar matsala ce ta haddasa hatsarin.
Tirelar na ɗauke da mutum 19, wanda 12 daga cikinsu suka rasu, sai wasu biyar da suka jikkata.
Mutum biyu ne kacal suka tsallake rijiya da baya ba tare da sun ji rauni ba.
An kai waɗanda suka jikkata Babban Asibitin Garin Kura, sannan an kai gawarwakin waɗanda suka rasu Asibitin Nasarawa.
Kwamandan FRSC na Kano, M.B. Bature, ya ziyarci wajen da hatsarin ya auku, inda ya zargi lodin kaya masu yawa da rashin bin dokokin hanya da haddasa hatsarin.
Ya gargaɗi direbobi kan haɗa kaya, dabbobi da fasinjoji a mota ɗaya.
A madadin Babban Kwamandan FRSC, Dauda Ali Biu, ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasu, tare da yi wa waɗanda suka jikkata fatan samun sauƙi.