Mutum 14 sun mutu, 50 sun jikkata a hatsarin jirgin kasa a Indiya

Mafi munin hatsarin jirgin kasa da aka samu a Indiya shi ne wanda ya faru a 1981.

Mutum 14 sun mutu, 50 sun jikkata a hatsarin jirgin kasa a Indiya

Akalla mutum 14 ne suka rasa rayukansu, sama da 50 kuma suka jikkata bayan wasu jiragen kasa biyu sun ci karo da juna a Kudancin Indiya, kamar yadda hukumomi suka bayyana a ranar Litinin.

Hatsarin ya faru ne a ranar Lahadi da yammaci bayan daya daga cikin jiragen kasan ya ki tsayawa a wurin da ya kamata tsakanin garuruwan Alamanda da Kantakapalle da ke Jihar Andhra Pradesh.

Binciken wucin-gadi da aka gudanar ya nuna cewa “matsala ce ta bil adama” ta jawo jiragen suka ci karo da juna, kamar yadda Ministan Sufurin Jiragen Kasa ya bayyana.

“Fasinjoji 14 sun rasu, wasu guda 50 kuma sun jikkata. Ana ci gaba da gudanar da ayyukan ceto,” kamar yadda wani babban jami’in gwamnati Nagalakshimi S. ya shaida wa manema labarai.

Shi ma Firaiministan Indiya Narendra Modi ya bayyana cewa ya yi magana da ministan sufurin jirigin kasa kan lamari mai takaici.

“Hukumomi na yin iya kokarinsu domin taimaka wa wadanda lamarin ya faru da su,” kamar yadda Modi ya shaida a kafofin sada zumunta.

Hatsarin jirgin kasa ya taba kashe mutum 800 a Indiya

Ana iya tuna cewa Indiya ce kasar da take da hanyoyin jirgin kasa mafi girma kuma an samu hatsarin jirgagen kasa da dama a tawon shekaru.

Mafi munin hatsarin jirgin kasa da aka samu a Indiya shi ne wanda ya faru a 1981, a lokacin da wani jirgin kasa ya sauka daga layin dogo a lokacin da yake tsallaka wata gada a Jihar Bihar, inda kusan mutum 800 suka rasu.

A watan Yuni, jiragen kasa uku suka yi karo inda kusan mutum 300 suka rasu a jihar Odisha.

A watan Agusta kuwa, akalla mutum tara suka rasu a lokacin da wani tarago wanda aka ajiye shi a kudancin Indiya ya kama da wuta a lokacin da wani fasinja ke son hada shayi.

Haka kuma a farkon watan nan, mutum hudu suka rasu bayan wani jirgi mai tsananin gudu ya sauka daga layin dogo a jihar Bihar.

An kai hari Fadar Shugaban Ƙasar Chadi

Ambaliyar Ruwa: Mutum 24 sun rasu, an tallafa wa magidanta 1,000 a Bauchi

’Yan sanda sun kama ’yan damfara 5 a Yobe

Nan ba da jimawa za a ƙara kuɗin kiran waya da data — Gwamnati