Mutum 143 ne suka warke daga cutar Ebola a Saliyo
Tun bayan barkewar annobar Ebola a watan Fabrairun da ya gabata, an fi raja’a ne kan yadda kwayar cutar take saurin kisa. Amma akwai mutane da dama wadanda suka kamu da cutar kuma suka warke.Wannnan ya sa a makon jiya wata ma’aikaciya da ke aiki da Asusun Tallafawa Yara na Majalisar dinkin Duniya (UNICEF) mai […]
Tun bayan barkewar annobar Ebola a watan Fabrairun da ya gabata, an fi raja’a ne kan yadda kwayar cutar take saurin kisa. Amma akwai mutane da dama wadanda suka kamu da cutar kuma suka warke.
Wannnan ya sa a makon jiya wata ma’aikaciya da ke aiki da Asusun Tallafawa Yara na Majalisar dinkin Duniya (UNICEF) mai suna Jo Dunlop, ta bayyana yadda ganawarta da wasu wadanda aka sallama daga wata cibiya da ke duba masu fama da cutar a garin Kenema da ke kasar Saliyo. A shafinta na Intanet, ta bayyana farin cikinta lokacin da ta samu labarin cewa wasu sun warke bayan harbuwarsu da kwayar cutar.
Ta ce: “Kafin wadanda aka sallama su bar cibiyar, ana ba su kudin motar da zai kai su gida wanda ya kai Dala 10 (kimanin Naira 1660) da sabbin sutura da takarda da take bayyana cewa mutum ya warke daga cutar Ebola,” Inji ta.
Hukumar UNICEF ta ce ana ci gaba da samun mutanen da ke warkewa daga cutar, wanda zuwa yanzu mutum 143 ne suka warke daga cikin 500 da suka harbu da kwayar cutar a kasar ta Saliyo. Wannan ya taimaka matuka a ci gaba da ayyukan wayarwa da al’umma kai da kuma kawo karhen jita-jitar da ake yadawa game da annobar.
daya da cikin mutanen da suka warke daga cutar Isata Konneh wadda aka sallama daga cibiyar. Matar ’yar shekara 35 ta bar asibitin cikin kwalla rike da shaidar da ke nuni da cewa ta kubuta daga cutar. “Na yi farinciki matuka kuma na gode wa Ubangiji da Ya nuna min wannan ranar da kuma yadda ya tadi kafaduna,” inji ta.
Yawancin wadanda suka harbu da kwayar cutar ma’aikatan asibiti ne saboda yadda suke mu’amala da marasa lafiyar da ke dauke da ita. Shida cikin ma’aikatan jinyar cibiyar garin Kenema sun rasa ransu daga cutar. Kodayake Fatmata Sesay ita ma ma’aikaciyyar cibiyar ce da ta shafe mako uku tana jinya sakamakon kamuwa da ta yi da cutar wanda hakan ya sa diyarta mai suna Tata ‘yar shekara 11 ita ma ta harbu. Fatmata ta ce a lokacin da aka tabbatar mata da cewa ita da diyarta sun warke daga cutar ta bayyana cewa “na ji kamar ni na fi kowa farin ciki a fadin duniya saboda yadda ba kowa ba ne yake samun sa’ar warke wa daga cutar. A lokacin da aka kawo ni wannan asibitin, ina zubar da jini ta hanci da baka amma ga shi yanzu na warke, komai ya zama labari” inji ta.
Kodayake, a shekaranjiya Laraba hukumar Raya Tattalin Arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) ta tabbatar da mutuwar wani jami’inta mai suna Jatto Asihu Abdulkadir,wanda shi ne mutum na uku da cutar Ebola ta hallaka a kasar nan. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin kasar Kanada ta ce za ta baiwa Hukumar Lafiya ta Duniya(WHO) tallafin maganin cutar mai suna ZMapp wanda yake kan matakin gwaji, a fatan samun nasara a yakin da ake da annobar.
Cutar Ebola ta hallaka mutane fiye da dubu daya a kasashen Guinea da Laberiya da Saliyo da kuma Najeriya.