Mutum 15 sun mutu bayan Jirgin sama ya fado kan wani gida a Kazakhstan
Wani jirgin sama da yi hadari ya fado kan wani gida a Kazakhstan, inda akalla mutum 15 suka mutu sannan wasu da dama suka jikkata. Jirgin dai na Bel Air ya taso ne daga Almaty da misalin karfe 7:05 na safe (01:05 GMT) birnin da ya fi kowanne girma a Kazakhstan, inda ya tunkari Nur-Sultan, […]
Jirgin saman da ya fado
Wani jirgin sama da yi hadari ya fado kan wani gida a Kazakhstan, inda akalla mutum 15 suka mutu sannan wasu da dama suka jikkata.
Jirgin dai na Bel Air ya taso ne daga Almaty da misalin karfe 7:05 na safe (01:05 GMT) birnin da ya fi kowanne girma a Kazakhstan, inda ya tunkari Nur-Sultan, babban birnin kasar to amma sai ya rikito jim kadan bayan tashinsa.
Jirgin saman yana dauke da fasinjoji 100, amma wasu rahotanni sun bayyana cewa, fasinjoji 60 ne suka tsallake rijiya da baya yayin da a yanzu haka suke karbar magani a asibiti.
