Mutum 16 sun mutu 27 sun jikkata a hatsarin tirela a Kaduna

Mutum 16 sun rasu, 27 sun samu raunuka a hatsarin tirela a hanyar Kaduna-Abuja

Mutum 16 sun mutu 27 sun jikkata a hatsarin tirela a Kaduna

Jami’an Hukumar Kiyaye Hatsarin Mota a bakin aiki

Hatsarin tirela ya yi ajalin mutane 16 yayin da wasu 27 suka samu a Jihar Kaduna.

Kwamandan Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) a jihar, Kabir Nadabo ya ce hatsarin ya aurke ne ranar Lahadi.

Nadabo ya ce wata tirela kirar DAF dauke da mutane 65 ce ta kwace ta fada a cikin wani rami da asuba.

Ya bayyana cewa hatsarin ya faru ne a kusa da kauyen Audu Jangwam a kan Babbar Hanyar Kaduna-Abuja.

Yana yi zargin hatsarin ya auku ne a sakamakon gudun wuce ka’ida da kuma gajiyar direba.

Ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) cewa an kai wadanda suka jikkata asibiti

Jami’an hukumar na aikin ceto domin kawar da motar, wadda ta barinta ya tare hanyar.