Mutum 17 ’yan gari daya sun rasu a hadarin mota
Mutum 17 ’yan gari daya sun rasu, yayin da takwas suka samu munanan raunuka a wani mummunan hadarin mota da ya auku a hanyar Sakkwato zuwa Ilaleh a ranar Lahadin da ta gabata.Direban kantar da ke dauke da mutanen da hadarin ya rutsa da su mai suna Abdulmalik Yunusa wanda yanzu haka ke kwance a […]

Mutum 17 ’yan gari daya sun rasu, yayin da takwas suka samu munanan raunuka a wani mummunan hadarin mota da ya auku a hanyar Sakkwato zuwa Ilaleh a ranar Lahadin da ta gabata.
Direban kantar da ke dauke da mutanen da hadarin ya rutsa da su mai suna Abdulmalik Yunusa wanda yanzu haka ke kwance a asibiti ya ce sun fito daga kauyen Unwala zuwa garin Ilelah ne saboda cin kasuwa, sai wani mutum a cikin wata karamar mota ya gitta musu, motar da yake ja kirar kanta ta kwace ta tarwatse da mutane da shanun da suke dauke da su.
Malam Abdulmalik Yanusa da ke kwance a asibitin kwararru na Sakkwato ya kara da cewa, “ban san yawan mutanen da ke cikin motata ba, amma na san mutanen kauyen Unwala 14 ne suka rasu, mu takwas na jinya, hudu a nan asibitin kwararrun, hudu a Asibitin Koyarwa na Usman danfodiyo, inda marigaya uku suka fito daga kauyen Hura-Girke, da ke kusa da Unwala.”
Direban ya ce ya fi shekara goma yana tuka mota a tsakanin Arewaci da Kudancin kasar nan amma bai taba samun hadari ba sai yanzu.
Amadu Yanusa, dan daya daga cikin mamatan a zantawarsa da Aminiya ya ce “Babana Alhaji Yanusa dan kamasho ne a kasuwar Ilelah da kanensa Malam Usman mai sayar da kwarya a kasuwar da kuma kanensu Garba mai sayar da nama da suke zaune a gida daya yanzu mutuwa ta dauke su a lokaci daya. Gidanmu sun girgiza da wannan mutuwar da ba su taba ganin irinta ba, motar ta lalace sosai ba yadda za a yi ta sake amfani, ba ma a garinmu nake kasuwancina ba aka kira ni na dawo kan wannan matsala.”
Wani tsoho Malam Muhammad Unwala mai shekara 60 da yake jinyar dansa da hadarin ya rutsa da shi ya ce “A tsawon shekaruna kauyenmu bai taba ganin tashin hankali kamar wannan ba, mun damu sosai sai dai muna fatar Allah Ya ba mu lada da hakurin jure rasa mutum 17 din a lokaci daya.”
Aminiya ta gano hadarin ya faru ne da misalin karfe 2:00 na rana a kauyen Sandaga kilomita 10 kafin shiga garin Ilelah a karamar Hukumar Ilelah ta Jihar Sakkwato
Shugaban karamar Hukumar Ilelah, Alhaji Garba Ilelah ya ce hukumarsa ta dauki matakan da suka kamata, kuma sun raba buhunan shinkafa da masara da kudi Naiar dubu biyar ga wadanda waki’ar ta shafa.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Sakkwato DSP Al-Mustafa Sani ya tabbatar da faruwar lamarin.