Mutum 18 sun rasu a rikicin manoma da makiyaya a Neja
Mazauna yankunan sun ce har yanzu ana ci gaba da kai musu hare-hare.
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Neja ta tabbatar da rasuwar mutum 18, sakamakon rikicin da ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya a Ƙaramar Hukumar Rafi ta jihar.
Yankunan da rikicin ya shafa sun haɗa da Anguwan-Baago, Kuwan-Kasa, Mararraban-Gwadaro da Tashan-Bako.
Kakakin rundunar, SP Wasiu Abiodun, ya ce mutane 15 sun ƙone ƙurmus a cikin wani gida da ke Anguwan-Baago.
Ya bayyana cewa rikicin ya fara ne a ranar 29 ga watan Yuni, sannan ya ƙara tsananta bayan hare-haren ramuwar gayya.
A cewar ‘yan sanda, wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka fara harbe Ibrahim Musa mai shekara 25 har lahira a ƙauyen Godoro.
Daga bisani, wasu ‘yan sa-kai suka tare hanya tare da kashe Bashir Mazi mai shekara 28 domin ramuwar gayya.
‘Yan sanda sun ce ana kyautata zaton rikicin na da alaƙa da tsohuwar taƙaddama kan mallakar ƙasa tsakanin ɓangarorin biyu.
Abiodun, ya ce zuwa ƙarfe 10 na daren ranar 1 ga watan Yuli, an kashe mutane 15 ta hanyar ƙone su a cikin wani gida, yayin da wasu uku suka mutu a wasu hare-hare daban, lamarin da ya kai adadin waɗanda suka rasu zuwa 18.
Ya ce kwamitin sulhu da Ƙaramar Hukumar ta kafa tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro na ci gaba da ƙoƙarin kawo ƙarshen rikicin.
Ya kuma ƙara da cewa an tura jami’an ‘yan sanda da sojoji zuwa yankin domin tabbatar da zaman lafiya.
Sai dai wasu mazauna yankin sun musanta adadin da ‘yan sanda suka bayar, inda suka ce waɗanda suka rasu sun fi haka yawa.
Sun ce hare-haren sun ci gaba har zuwa ranar Alhamis, inda aka ƙone garin Tashan-Bako gaba ɗaya.
Wani shugaban al’umma ya ce har yanzu ana ci gaba da kashe mutane, kuma ba za a iya tantance ainihin adadin waɗanda suka rasu ko jikkata ba saboda rashin damar isa yankunan da abin ya shafa.
Ya kuma yi zargin cewa jami’an tsaro ba su isa yankin ba, duk da iƙirarin da ‘yan sanda suka yi.
A cewarsa, mata da yara da sauran mazauna yankin sun tsere zuwa Tegina, Maikujeri, Pandogari, Kagara da sauran garuruwan da ke kusa da yankin.
Wani mazaunin yankin ya yi zargin cewa sama da mutane 30 aka ƙone a gidajensu, yayin da wasu da dama suka jikkata.
Ya kuma zargi hukumomi da gaza ɗaukar matakin gaggawa domin daƙile rikicin.