Mutum 182 sun mutu a hatsarin kwalekwale a Neja a shekaru uku —Bago
Gwamna Bago ya yi kira da a tsaurara dokar sufurin ruwa domin kare rayuka da dukiyoyi
Mutane 182 ne suka rasu a sakamakon hatsarin kwalekwale a Jihar Neja daga shekarar 2022 zuwa 2024.
Gwamna Mohammed Umaru Bago, ya ce hatsarin kwalekwale ya yi ajalin mutane 95 a shekarar 2022, da wasu 68 a 2023 sannan aka samu 19 a 2024.
Ya bayyana hakan ne ta bakin mataimakinsa Yakubu Garba, a wajen bikin Ranar Ruwa ta Duniya ta 2024, da kuma rabon jiragen ruwan zamani da Hukumar N-HYPPADEC ta gudanar a Minna.
Gwamna Bago ya yi kira da a tsaurara dokar sufurin ruwa domin kare rayuka da dukiyoyi.
Tun da farko, Manajan Daraktan, N-HYPPADEC, Abubakar Sadiq Yelwa, ya ce jiragen ruwan zamani sun fi na katako kariya.
Ya danganta yawan hatsarin kwalekwale a Jihar Neja da yawaitar bishiyoyi a cikin ruwa, da yawan lodi fiye da ƙima da kuma tafiye-tafiyen dare.
Ya ce hukumar ta taimaka wajen rage yawan asarar rayuka a sakamakon hatsarin kwalekwale da suka hada da raba rigunan kariya da sauransu.
Yelwa ya ce jihohin Kaduna da Gombe za su samu kwalekwalen zamani guda ɗaya kowannensu, Nasarawa da Taraba kuma za a ba su biyu-biyu.
Binuwai za ta samu uku, Kwara da Kogi za su samu huɗu-huɗu, Kebbi shida, a yayin da Neja za ta samu takwas.
Ya bayyana cewa an yi rabon ne bisa la’akari da rafukan da ke jihohin da abin ya shafa.
Shugaban masu sufuri da kwalekwale na Jihar Neja, Alhaji Attahiru Isah, ya yi kira da a samar da jami’an ceto domin ɗaukar matakin gaggawa a duk lokacin da hadurra da suka faru.