Mutum 2 sun mutu a gobarar tankar mai a Legas
Rahotanni na bayyana cewa, mutum biyu mace da namiji sun rasa ransu sanadiyyar gobarar tankar man fetur wanda ta dauko litar man fetur dubu 33 ta fadi ta kama da wuta a barikin tashar mota da ke Mil 2 zuwa Badagry a Jihar Legas. Wani ganau ya ce, lamarin ya faru ne da misalin karfe […]
Rahotanni na bayyana cewa, mutum biyu mace da namiji sun rasa ransu sanadiyyar gobarar tankar man fetur wanda ta dauko litar man fetur dubu 33 ta fadi ta kama da wuta a barikin tashar mota da ke Mil 2 zuwa Badagry a Jihar Legas.
Wani ganau ya ce, lamarin ya faru ne da misalin karfe 5 na asubahin ranar Laraba.
Manyan motoci biyu da kananan motoci uku ne suka kone kurmus.
Jama’in hulda da jama’a na hukumar ‘yan sandan jihar Legas Emeka Oti ya tabbatar da aukuwar lamarin, wadanda suka rasun su na cikin wadanda suka mallaki motocin.