Mutum 2 sun rasu, 37 sun jikkata a benen da ya rushe a Abuja

An kokarin ceto ragowar mutanen da suka makale a cikin baraguzan baraguzan ginin da ya rushe a unguwar Garki Village da ke Abuja.

Mutum 2 sun rasu, 37 sun jikkata a benen da ya rushe a Abuja

Ana fargabar mutum biyu sun mutu wasu sama da 37 sun samu ranuni sakamakon rushewar wani bene a yankin Babban Birnin Tarayya, Abuja.

An garzaya asibiti da mutun 37 da aka ciro daga baraguzan ginin da ya rushe a unguwar Garki Village da ke Abuja.

Ikharo Atttahh, Hadimin tsohon ministan Abuja, Mohammed Bello ya tabbatar da alkaluman mamatan da wadanda suka samu rauni, inda ya wallafa bidiyon al’a,amarin.

A halin yanzu masu aikin ceto na kokarin ciro ragowar mutanen da suka makale a cikin baraguzan ginin da ibtila’in ya auka masa a cikin daren Laraba.

Wani mazaunin yankin Garki ya tabbatar mana da faruwar lamarin amma bai yi karin bayani ba.

Kawo yanzu dai hukumomi ba su ce komai game da lamarin, wanda shi ne rushewar gini na farko, kwana biyu bayan fara aikin sabon minista, Nyesom Wike.

Za a iya tunawa a jawabin Wike na karbar rantsuwa ya yi alkawarin rushe duk gine-ginen da aka yi ba bisa ka’ida ba a birnin.

 

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan