Mutum 2 sun rasu, 6 sun jikkata yayin da gini ya rufta a Legas
Hukumomi na bincike domin gano musababbin ruftawar ginin.

Wani gini mai hawa biyu ya rufta a yankin Lekki da ke Jihar Legas wanda ya yi sanadin mutuwar mutum biyu tare da jikkata wasu shida.
Jami’an bayar da agaji daga hukumomin LASEMA da NEMA sun ceto waɗanda suka jikkata kuma an kai su Babban Asibitin Marina domin kula da lafiyarsu.
- Majalisar Kano ta yi wa dokar hukumar tace fina-finai gyaran fuska
- Kwamitin majalisa ya yi watsi da ƙorafin Natasha a kan Akpabio
Tun da farko, ’yan sanda sun ce an ceto mutum 14 daga wajen da ginin ya rufta.
Sakataren hukumar LASEMA, Dokta Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya bayyana cewa ana bincike don gano musabbabin rushewar ginin.
“Zuwa yanzu mun gano gawarwakin mutum biyu daga cikin baraguzan gini, yayin da aka kai mutum shida da suka jikkata zuwa asibiti,” in ji shi.
“Ana ci gaba da gudanar da ayyukan ceto domin gano waɗanda lamarin ya rutsa da su.”