Mutum 2 sun shiga hannu kan safarar yara 16 a Taraba
An cafke mutanen yayin da suke shirin safarar yaran zuwa Jihar Edo.
Jami’an tsaron hukumar Sibil difens (NSCDC) sun cafke wasu mutum biyu da ake zargi da safarar kananan yara 16 a Jihar Taraba.
Wadanda ake zargin sun shiga hannu ne a ranar Alhamis a Jalingo tare da kananan yara 16 da suke kokarin safarar su zuwa Jihar Edo.
- Wani abu ya yi bindiga da dalibin Islamiyya a Kaduna
- NAJERIYA A YAU: Dabaru 10 Na Kaucewa Masu Garkuwa Da Mutane
Kwamandan NSCDC na jihar, Adamu Salihu ne, ya ce yaran wadanda shekarunsu ya kama daga 10 zuwa 16, mata biyar da maza 11, an sato su ne daga Kananan Hukumomin Zing da Bali na jihar.
Kwamandan, ya shaida wa manema labarai a ranar Asabar a Jalingo cewa bincike ya nuna cewa wadanda ake zargin suna cikin wata kungiya da ta kware wajen safarar kananan yara ne.
Saliuhu ya ce akan tilasta yaran wajen yin aikatau da ke jefa su cikin rayuwar matsi har da karuwanci a wasu lokutan.
Ya koka kan yadda iyaye ke kasa sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na kula da ’ya’yansu, inda suke bai wa wasu da sunan kai su aikatau.
“Ta yaya mutum zai haifi ’ya’ya kuma ya sa ran wasu su dauki nauyin ciyar da su, sutura, ilimi, da walwalarsu baki daya?
“Yawancin yaran da aka kwaso daga jihar ana sayar da su ne don yin karuwanci yayin, wasu kuma ana amfani da su a matsayin masu samar da jarirai.
“Da yawan yaran da ake sacewa kanana ne da su wuce a ce suna makarantar Firamare ba, amma iyayensu sun gaza ba su kulawar da ta dace,” in ji shi.
Kwamandan ya kara da cewa, “Dole ne a kawo karshen safarar kananan yara a jihar nan da ma Najeriya baki daya.”
An mika wadanda ake zargin tare da yaran 16 ga jami’an Hukumar Yaki da Fataucin Mutane ta Kasa (NAPTIP), domin ci gaba da bincike.