Mutum 20 da Shata ya fito da su a waka

Aminiya ta tuntubi marubucin littafin tarihin Shata, Dokta Aliyu Ibrahim Kankara, malami a Sashen Nazarin Kimiyyar Duwatsu a Jami’ar Tarayya ta Dutsin-ma, wanda ya zayyano fitattun mutane 20 da ya tantance, wadanda kuma marigayi Mamman Shata ya yi masu waka: 1-Sarkin Daura Mamman Bashar: Ya san Shata tun 1948 a Bakori kuma ya yi masa […]

Mutum 20 da Shata ya fito da su a waka
Mutum 20 da Shata ya fito da su a waka

Aminiya ta tuntubi marubucin littafin tarihin Shata, Dokta Aliyu Ibrahim Kankara, malami a Sashen Nazarin Kimiyyar Duwatsu a Jami’ar Tarayya ta Dutsin-ma, wanda ya zayyano fitattun mutane 20 da ya tantance, wadanda kuma marigayi Mamman Shata ya yi masu waka:

1-Sarkin Daura Mamman Bashar: Ya san Shata tun 1948 a Bakori kuma ya yi masa wakoki har 13.

2-Bello Maitama Yusuf: Ya san Shata tun cikin 1972. Ya zama ubangidansa a 1979 kuma ya yi masa wakoki 71.

3-Usman Liman Durbi: Shi ne Hakimin Musawa (1939-1963). Ubangidan Shata ne tun a 1940 kuma ya yi masa wakoki da dama.

4-Inuwa Mammada Dan Sambo: Ya san Shata a 1940 kuma ubangidansa ne na farko. Ya yi masa waka guda daya amma tana da rassa.

5-Bawa Direba: Ya san Shata tun 1936 amma sai a 1947 ya yi masa waka, lokacin bikinsa a Katsina.

6-Umaru Danduna: Ya san Shata tun yana matashi amma sai a 1971 ya yi masa waka.

7-Sani Audi: Shata ya yi masa wakoki a 1950, a Batsari, lokacin yana Malamin Kada. Ya yi masa wata wakar 1970, lokacin yana aikin Kwastam.

8-Garkuwan Bauchi Amadun Kari: Ya san Shata a 1952, lokacin yana karatun Diploma kan Aikin Gona a Samaru Zariya. Sun san juna a Kano cikin 1963, lokacin Kari yana Sakataren Tafawa Balewa a Kano amma sai a 1971 ya yi masa waka.

9-Hauwa Mai Tuwo Matar Lado: Ta fara son Shata tun tana karama. Ya yi mata waka cikin 1976 a Kano.

10-Indo Kyaftin Zariya: Ta fara sanin Shata a watan Janairun 1943, a Zariya. Ya yi mata waka daya, ta ‘Haka nan ne Mamman…’ amma ya raba ta kashi-kashi.

11-Umaru Chiroman Gombe: Ya san Shata cikin 1966, a Gombe. Ya yi masa waka a shekarar. Da ya rasu ma ya yi masa wata wakar ta ta’aziyya a 1975.

12-Aliyu Lamidon Adamawa: Shata ya yi masa waka a 1979 a Yola.

13-Ja’e Dan Ali: Yana Mararrabar Daudawa kuma ya yi masa waka a 1975. Ya san Shata tun cikin 1970.

14-Haruna Dan Kasim: Ya kai Shata Makka cikin 1956, ya yi masa waka a 1955 a Kano.

15-Sufeto Yusufu Shema Dandoka: Ubangidan Shata na wani lokaci. Ya yi masa waka a 1955 a Katsina.

16-Kilishi Jikar Dikko: Shata ya yi mata waka a 1964, lokacin da ta auri Wamban Daura Bashar.

17-Alhaji Sani Store: Ubangidan Shata ne na lokaci mai tsawo. Ya yi masa wakoki uku a Katsina.

18-Hajiya Inno Ahmadu: Ya yi mata waka cikin 1974.

19-Alhaji Balan Goggo: Ya yi masa waka cikin 1965 a Katsina kuma ubangidansa ne na lokaci mai tsawo.

20-Wili Dan Usman Salgare: Ya san Shata cikin 1968 kuma ya yi masa wakoki kusan shida.

Tinubu ya yaba wa NNPCL kan fara aikin Matatar Warri

Masu son Abba ya tsaya da ƙafarsa za su cuce shi – Kwankwaso

Matatar Warri ta fara aiki bayan shekara 9

’Yan sara-suka sun yi wa tela kisan gilla a Jos