Mutum 20 sun tsere daga Cibiyar Horar da Nakasassu ta Abuja

Wasu daga cikin waɗanda aka kama tare da tsare su a Cibiyar Horar da Nakasassu ta Birnin Tarayya Abuja da ke ƙauyen Kuchiko da ke bayan garin Bwari Abuja, sun tsere daga wajen. Wasu al’umman yankin da suka zanta da Aminiya sun bayyana cewa, waɗanda suka tseren da ba za su gaza mutum 20 ba, […]

Mutum 20 sun tsere daga Cibiyar Horar da Nakasassu ta Abuja

Wasu daga cikin waɗanda aka kama tare da tsare su a Cibiyar Horar da Nakasassu ta Birnin Tarayya Abuja da ke ƙauyen Kuchiko da ke bayan garin Bwari Abuja, sun tsere daga wajen.

Wasu al’umman yankin da suka zanta da Aminiya sun bayyana cewa, waɗanda suka tseren da ba za su gaza mutum 20 ba, sun gudu daga wajen ne a daren Lahadin da ta gabata, inda suka nemi taimakon abinci da kuma takalma daga jama’ar da suka haɗu da su a yayin tserewar tasu.

Ɗaya daga cikin majiyoyin ya ce, mutanen da suka tseren sun nuna cewa, sun fuskanci matsalar rashin ciyarwa da musgunawa bayan kama su da kuma zamansu a wajen. Aminiya ta ba da labarin yadda mabarata ke ci gaba da wasan ɓuya a tsakaninsu da jami’an duba gari na Abuja da ke kama su a kan titunan tare da jefa su a motoci na a-kori-kura, tun bayan cikar wa’adi da Ministan Birnin Tarayya Abuja, Mista Nyesom Wike ya bayar, kan su bar yankin ko kuma su fuskanci kamu.

Bayan cikar wa’adin a ranar Litinin ta makon jiya, ayarin jami’an waɗanda ke samun rakiyar jami’an tsaro ciki har da sojoji, sun yi ta kama mabaratan tare da masu sana’ar bola-jari da kuma masu taɓin hankali.

Bayanai sun ce, waɗanda suka gudun sun tsere ne ta katangar bayan gidan a maimakon bi ta mashigarta, inda jami’an tsaro da aka ƙara adadinsu a cibiyar suka fi mai da hankali a kai.

Yunƙurin wakilinmu na jin ta bakin jami’an da ke wajen a kan lamarin bai samu nasara ba, a lokacin da ya kai ziyara a ranar Asabar da ta gabata, inda suka ce hakan ya saɓa wa dokar aiki har sai idan sun samu izini tukuna. Sai dai a bayanin da babban jami’i da ma’aikatar Birnin ta naɗa don aiwatar da dokar kamen, Mista Peter Olumiji ya ƙaryata aukuwan lamarin, sannan ya ce an ƙarfafa tsaro a wajen.

Ya ce, “Hukumar Tabbatar da Walwalar Jama’a ta Abuja ce ke da alhakin ciyar da waɗanda aka tsare da su tare da ba da horon sana’a ga masu sha’awa ko kuma mayar da su zuwa yankunansu na asali ga masu buƙatar hakan.” In ji shi.

Mun kusa kawo ƙarshen rikicin manoma da makiyaya — Tinubu

Tsohon shugaban jam’iyyar PDP na Gombe, ya rasu

Matatar Dangote ta rage farashin man fetur 

Na kusa zama ɗan ƙwaya a baya — Obasanjo