Mutum 2000 sun bar garuruwansu sakamakon janye jami’an tsaro a Zamfara

Mazauna garuruwan na fargabar mahara na iya kai musu hare-haren ɗaukar fansa.

Mutum 2000 sun bar garuruwansu sakamakon janye jami’an tsaro a Zamfara

Sama da mutum 2000 ne, suka tsere daga muhallansu sakamakon janye jami’an tsaro daga wasu yankuna a Jihar Zamfara.

Ɗaya daga cikin mazauna ƙauyen mai suna Muhammad Murtala, ya bayyana wa manema labarai cewa hakan ya zame musu dole domin tseratar da rayukansu daga halaka.

“Dukkanin jami’an tsaron da aka jibge a sassa daban-daban na garuruwan sun bar wuraren bayan sun samu nasara a kan ’yan bindiga kwanaki biyu da suka gabata,” in ji shi.

Al’ummar garin Kunchin Kalgo da sauran maƙwabtansu na daga cikin garuruwan da mutane suka haɗa kayansu suka yi ƙaura zuwa hedikwatar Ƙaramar Hukumar Tsafe.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Tsafe, Garba Shehu Fanchers, ya tabbatar wa wakilinmu batun kwararar ’yan gudun hijira zuwa hedikwatar.

Sai dai ya bayyana cewa jami’an sa-kai sun bar garuruwan ne domin kammala shirye-shiryen canjin wajen aiki da aka yi musu.

Ya ƙara da cewa: “Mutane na ta guduwa daga garuruwansu ne saboda jita-jitar da ake yaɗawa, amma labaran ba gaskiya ba ne.”

Hakazalika, ya bayyana cewa duk da janye wasu, har yanzu akwai sauran jami’an tsaro a wasu sassan yankin.

Mazauna ƙauyukan sun ce suna barin garuruwansu ne saboda fargabar cewa ’yan bindigar na shirin kai hare-haren ɗaukar fansa.