Mutum 21 sun mutu bayan motarsu ta fada a cikin tafki

Mutum 21 sun rasu wasu 15 kuma sun samu raunuka sakamakon hadarin da motar da suke ciki ta yi ta kuma fada a cikin tafki. Lamarin ya auku ne a birnin Anshun da ke Kudu maso Yammacin lardin Guizhou na kasar China a ranar Talata, a cewar hukumomin kasar. Kamfanin dillancin labarun kasar China, Xinhua, […]

Mutum 21 sun mutu bayan motarsu ta fada a cikin tafki

Ana aikin tsamo motar daga cikin ruwa a Anshun da ke lardin Guizhou na kasar China

Mutum 21 sun rasu wasu 15 kuma sun samu raunuka sakamakon hadarin da motar da suke ciki ta yi ta kuma fada a cikin tafki.

Lamarin ya auku ne a birnin Anshun da ke Kudu maso Yammacin lardin Guizhou na kasar China a ranar Talata, a cewar hukumomin kasar.

Kamfanin dillancin labarun kasar China, Xinhua, ya ce jami’an ceto na kokarin tsamo matar daga cikin ruwan da ta fada.