Mutum 213 sun sake kamuwa da COVID-19 a Najeriya —NCDC
An sami mutanen ne a wasu jihohi 12
Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa (NCDC) ta ce, an samu karin mutum 213 da suka kamu da cutar COVID-19 a fadin Najeriya.
Hukumar ta sanar da hakan ne a shafinta na Telegram a ranar Alhamis.
- Gwamnan Neja ya dakatar da shugaban hukumar ilimin bai daya
- Matasa 42 sun mutu bayan sun yi tatul da gurbatacciyar giya a Indiya
Ta ce karin da aka samu ya shafi wasu jihohi 12 ne da suka hada da Edo mai mutum 77, Oyo 32, Kaduna-27, Ribas 27, Delta 13, sai kuma Kano mai mutum tara.
Sauran sun hada da Kuros Riba mai mutum bakwai, Imo bakwai, Ekiti shida, Sakkwato hudu, Bayelsa biyu, da kuma Nasarawa ita ma mutum biyu.
NCDC ta ce ya zuwa yanzu, mutum 260,977 aka tabbatar sun harbu da cutar a fadin kasa, yayin da 253,690 sun warke an kuma sallame su, sannan cutar ta yi ajalin mutum 3,147 a fadin kasa.