Mutum 22 sun mutu a ruftuwar ginin makaranta a Jos

An bukaci duk wasu makarantun da da ba su tabbatar da ingancin gininsu ba da su rufe nan take.

Mutum 22 sun mutu a ruftuwar ginin makaranta a Jos

Aƙalla mutum 22 galibi ɗalibai ne suka mutu bayan ruftawar gini mai hawa biyu a wata makaranta a birnin Jos da ke Jihar Filato.

Aminiya ta ruwaito cewa, a safiyar ranar Juma’a ne ginin makarantar Saint Academy da ke unguwar Busa Buji a Karamar Hukumar Jos ta Arewa ya rufta a kan ɗaliban da ke rubuta jarrabawa kamar yadda gwamnatin Jihar Filato ta tabbatar.

Kazalika mutum 132 da suka jikkata sakamakon ruftawar ginin na samun kulawa a asibitoci daban-daban da ke birnin Jos in ji wata sanarwa da Kwamishinan Watsa Labarai na jihar Musa Ibrahim Ashoms ya fitar ranar Juma’a da maraice.

Hukumomin bayar da agajin gaggawa daban-daban da suka hada da ta kasa NEMA da ta jiha SEMA da kuma ta kasa-da-kasa Red Cross da jami’an tsaro ne suka rika fadi tashin zakulo ɗaliban da suka maƙale a ƙarƙashin baraguzan ginin.

Tuni dai Gwamna Caleb Mutfwang ya jajanta wa dukkanin wadanda abin ya shafa kama daga mahukuntan makarantar, iyayen ɗalibai da kuma al’ummar Jihar Filato baki daya dangane da wannan mummunan iftila’in da ya auku.

Gwamnan ya kuma jaddada mahimmancin bin ka’idojin tabbatar da ingancin gine-gine, inda ya bukaci duk wasu makarantu da sauran wuraren da ba su tabbatar da ingancin ginin da suke ciki ba da su rufe nan take.

NCC ta amince wa kamfanonin sadarwa ƙara kuɗin kira da data

Amurka jinsin mace da namiji kaɗai ta sani a hukumance — Trump

An rantsar da Donald Trump a matsayin Shugaban Amurka na 47

Za mu yi gwanjon motoci 891 da muka ƙwace — EFCC