Mutum 24 sun rasu a harin masallaci a Maiduguri
Wadansu ’yan kunar bakin wake da ake zargin ’yan Boko Haram ne sun kashe akalla mutum 24 a lokacin da suke Sallar Asuba a wani masallaci da ke yankin Umarari a kusa da birnin Maiduguri a shekaranjiya Laraba. A Kuma mutum 35 sun jikkata a harin da aka kai a masallacin na Umarari- Molai da […]
Wadansu ’yan kunar bakin wake da ake zargin ’yan Boko Haram ne sun kashe akalla mutum 24 a lokacin da suke Sallar Asuba a wani masallaci da ke yankin Umarari a kusa da birnin Maiduguri a shekaranjiya Laraba. A Kuma mutum 35 sun jikkata a harin da aka kai a masallacin na Umarari- Molai da ke da nisan kilomita shida daga birnin Maiduguri fadar Jihar Borno.
Kakakin Rundunar Sojin Najeriya, Kanar Sani Usman Kukasheka a cikin wata sanarwa ya ce mata ’yan kunar bakin wake ne suka kai hari a masallacin na Umurari, kuma ya tabbatar da mutuwar mutum 22 a harin, a yayin da wasu fiye da 18 suka samu raunuka. A cewar sojin, an tura karin dakaru zuwa yankin domin bayar da kariya.
Wani mai aikin ceto ya ce sun kwashe gawarwaki 24 da wadanda suka samu rauni 35 zuwa asibitin kwararru na jihar. “daya daga cikin gawarwakin da aka ciro daga masallacin na wata mace ce. Kuma mun samu gawar wata mace a waje. Ana da yakinin gawarwakin na wadanda suka kai harin ne,” inji shi.
Limamin Masallacin, Malam Gwani Kyari ya shaida wa BBC cewa bam na farko ya tashi ne tun kafin su yi raka’ar farko a lokacin Sallar. “Bam din farko ya tashi ne kafin mu yi raka’ar farko, sannan na biyu ya tashi a wajen masallacin,” in ji Liman Gwani.
Wannan hari yana zuwa ne a daidai lokacin da sojojin Najeriya ke ci gaba da share sansanonin ’yan Boko Haram domin kawar da su daga yankin a Arewa maso Gabas, inda a ranakun Talata da Larabar da suka gabata, sojojin suka rusa sansanonin ’yan ta’addan na garuruwan Golgore da Bulasari a Jihar Yobe.
A cewar Kanar Kukasheka sojoji sun kashe ’yan ta’adda da dama yayin da soja daya ya samu raunin harbi kuma yana samun sauki.
Ya ce a yayin wannan aiki na kawar da mayakan Boko Haram, sojojin sun kwato wata motar yaki da ’yan ta’addan suka sace lokacin da suka kai hari a ranar 9 ga Yulin bara a garin Buni Yadi.