Mutum 25 rasu, gidaje 312,000 sun rushe sanadiyyar ambaliya a Kebbi
Ƙananan hukumomi 5 daga cikin 21 na jihar ne kaɗai abin bai shafa ba
Gwamnatin Kebbi ta ce aƙalla an yi asarar rayukan mutane 29 da gidaje 321,000 da gonaki 858,000 sanadiyyar ambaliyar ruwa a ƙananan hukumomi 16 daga cikin 21 na jihar.
Kwamishinan Labarai, Yakubu Ahmed Birnin Kebbi ne bayyana hakan a ranar Juma’a a yayin zantawa da manema labarai a cibiyar manema labarai da ke Birnin Kebbi.
- Harin Offa: Kotu ta yanke wa ’yan fashin banki hukuncin kisa
- Sojoji sun kashe shugabannin ’yan bindiga 65 da mayaƙa 1,937 a watanni uku
Ya ce, idan ba ɗauki mataki a yankunan da abin ya shafa ba, wanda suka rasa shinkafa da Masara da dawa da sauran amfanin gona da ambaliyar ta lalata za a iya samun ƙarancin abinci a jihar da kasar.
Ya ce, kafin gargaɗin da Hukumar Hasashen Yanayi NIMET ta yi, jihar ta fuskanci ibtila’i mai tsanani sakamakon ambaliya a ƙananan hukumomi 16 na jihar a dalilin ruwan da aka sako daga Madatsar Ruwa ta Goronyo da kuma magudanar ruwa a kogin Rima da kogin kaa da ke kwararo tun daga Kogin Neja.
Kwamishinan ya ce duk da matakan da gwamnatin ta ɗauka har yanzu jihar na fama da ambaliyar ruwa a ƙananan hukumominta 16.
“Kananan hukumomi 5 daga cikin 21 na jihar ne kaɗai abin bai shafa ba. Ambaliyar ta lalata gonaki, gadoji da dubban gidaje.
“Game da adadin wadanda suka mutu, mun rasa mutane bakwai a Shanga, takwas a Maiyama, biyar a Kalgo. Kazalika, an rasa mutum bakwai a Jega, biyu kuma a Birnin Kebbi,” in ji shi.