Mutum 25 sun mutu sanadiyar ambaliyar ruwa a Jigawa

Ambaliyar ruwa ta lalata gonaki da faɗinsu ya kai hekta 3,926 a jihar.

Mutum 25 sun mutu sanadiyar ambaliyar ruwa a Jigawa

Ambaliyar ruwa da mamakon ruwan sama ya haddasa, ta yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 25 a Jihar Jigawa.

Babban Daraktan Hukumar Agajin Gaggawa na jihar Jigawa, Dakta Haruna Mai Riga ne ya shaida wa BBC hakan a ranar Jumaa.

Ya bayyana cewa, a kullum adadin waɗanda ke mutuwa sakamakon ambaliyar ruwan na ƙaruwa saboda mamakon ruwan saman da ake na janyo gidaje na ruftawa wani lokacin a kan mutane.

Ya ce, baya ga asarar rai, ambaliyar ruwan ta lalata gonaki da faɗinsu ya kai hekta 3,926 a sassa daban-daban na jihar.

Dakta Mai Riga, ya ce,“Ambaliyar ruwan ta sa mutane 17,732, sun rasa muhallansu a ƙanana hukumomin da suka haɗar da Auyo da Buji da Gwaram da Garki da Kirika Samma da Maigatari da Kafin Hausa da Malam Madori da Haɗeja da Kiyawa da kuma Jahun.”

Shugaban hukumar ya ce a yanzu hukumarsu da kuma gwamnatin jihar na ƙokari wajen taimaka wa waɗanda ambaliyar ta shafa.

“Mun kai kayan agaji wasu yankunan kamar katifa da gidan sauro da kuma kayan abinci.”

Ya ce, a yanzu an tsugunnar da waɗanda ambaliyar ta shafa ko rusa wa gidaje a makarantun da ke garuruwan.

Dakta Mai Riga, ya ce jama’a su kwantar da hankulansu, hukumarsu dama gwamnatin jihar tana sane da halin da suke ciki