Mutum 25 sun rasu, 53 sun ji rauni a hatsarin mota a Kano

Hatsarin ya faru ne sakamakon gudun wuce ƙima da tirelar ke yi.

Mutum 25 sun rasu, 53 sun ji rauni a hatsarin mota a Kano

Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC) a Jihar Kano, ta tabbatar da rasuwar wasu matafiya 25, yayin da wasu 53 suka jikkata a wani hatsari da auku da sanyin safiyar ranar Litinin.

Hatsarin ya faru ne a kasuwar Ɗangwaro da ke birnin Kano.

Matafiyan na cikin wata tirela ne wadda ta ke ɗauke da shanu kuma ta nufi zuwa Kudancin Najeriya daga Maiduguri, inda ta yi karo da wata motar.

A cewar Kwamandan hukumar a jihar, Ibrahim Abdullahi, hatsarin ya faru ne tsakanin tirela (IVECO) mai lamba XA 311 ZB.

“Mun samu kiran waya da misalin ƙarfe 3:15 na safe a ranar 1 ga watan Yuli, 2024. Bayan samun labarin muka aike jami’anmu zuwa wajen da hatsarin ya faru domin ceto waɗanda hatsarin ya rutsa da su da misalin ƙarfe 3:30 na safe,” a cewar Ibrahim.

Kwamandan ya ce hatsarin ya faru ne sakamakon gudun wuce ƙima da kuma lodi fiye da ƙa’ida wanda ya haifar da hatsarin.

Ya ƙara da cewar a lokacin aikin ceto, jami’an hukumar sun samu babura guda shida, wayoyin hannu guda 10, dabbobi (akuyoyi da raguna), masara da kuma kuɗi Naira 400,000.

“An kai waɗanda suka ji rauni asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano, domin ba su agajin gaggawa. Likitocin da ake aiki sun tabbatar da mutuwar mutum 25 a cikin waɗanda hatsarin ya rutsa da su,” a cewarsa.

Ya gargaɗi masu ababen da su guji lodin mutane da kaya da dabobbi a lokaci ɗaya.

’Yan sanda sun ƙwace sakamakon zaɓe a Ribas

Yadda mutanen Jigawa suka ƙi fita zaɓen ƙananan hukumomi 

Za mu yi wa Kwankwaso ritaya a 2027 — Doguwa

’Yan daba sun ƙone ofishin hukumar zaɓen Akwa Ibom