Mutum 25 sun rasu bayan bullar sabuwar Annoba a Sakkwato
Kwamishinar Lafiya ta Jiha Sakkwato, Hajiya Asabe Balarabe ta bayyana cewa mutum 1, 160 ne annobar ta sama, amma 25 daga cikinsu sun rasu, wasu 15 suna asibiti.
Wata sabuwar annoba das ta bula a Sakkwato ta yi sanadin rasuwar mutane 25 tare da kwantar da wasu da dama a asibiti.
Kwamishinar Lafiya ta Jiha Sakkwato, Hajiya Asabe Balarabe ta bayyana cewa mutum 1, 160 ne annobar ta sama, inda 25 suka suka rasu, wasu 15 suna asibiti.
Kwamishiniyar ta kara da cewa lamarin ya faru ne a kananan hukumomi uku, Sakkwato ta Arewa da Silame da Kware.
Dan majalisa mai wakiltar Sakkwato ta Arewa ta Xaya a majalisar dokokin jiha, Buhari Haliru ya ce, ce annobar ta kashe mutum 7, wasu 95 kuma an kwantar da su a Koyarwa ta Jami’ar Usman Danfodiyo da Babbar Asibiti Kwararru ta Jihar Sakkwato da kuma karamin asibitin unguwar Bazza da ke Kofar Rini.
- Musabakar Al-Kura’ni: An karrama Gwarazan Shekara na Jihar Kogi
- Lakurawa: Yadda sojoji ke aikin murkushe ’yan ta’adda
“Gwamnati ta tura karin ma’aikatan lafiya a wuraren zaman da cutar ta bulla. A Kuma bibiyi silar bullar cutar don daukar mataki,”in ji shi.
A unguwar Gidadawa a Karamar Hukumar Sakkwato ta Arewa da aka samu bullar cutar, wani mazauni unguwar ya shaida wa wakilinmu cewa “babu wanda ya san dalilin bullar cutar.
“Amma ana zargi ruwan famfo ne ya haddasa lamarin, abin da ya kawo katse ruwa a unguwar gaba daya daga babban layin ruwa na jiha, ana ganin cutar Kwalara ce aka samu.”
Kwamishinar Lafiya ta Jiha Sakkwato, Hajiya Asabe Balarabe ta shaida wa manema labarai a ranar Litinin cewa ana ci gaba da bincikar wadanda aka samu da cutar don sanin ko Kwalara ce da daukar matakin da yakamata.
“Mutanenmu sun yi aiki sosai na ganin cutar ba ta watsu a wasu wurare ba.
“Gwamnatin jiha ba ta yi kasa a guiwa ba nan take ta sayo tare da raba magani a kananan hukumomi 18 don tabbatar da an dakile yaduwar cutar,” a cewar ta.