Mutum 28 sun musulunta a wurin wa’azin Izala na Bauchi

Mutum 28 ne suka musulunta a wurin wa’azin kungiyar Jama’atu Izalatul Bid’ah Wa Ikamatis Sunnah na kasa da ta gudanar a garin Miya da ke karamar Hukumar Ganjuwa a ranar Asabar da Lahadin da suka gabata.A jawabin shugaban Majalisar Malamai ta kasa ta kungiyar Sheikh Sani Yahaya Jingir ya ce za su tallafa da kayan […]

Mutum 28 sun musulunta a wurin wa’azin Izala na Bauchi

Daga dama Ustaz Salisu Sulaiman Ningi da Shugaban Majalisar Jihar Bauchi Alhaji Yahya Mohammed Miya a wurin wa’azin Izala na kasa a garin MiyaMutum 28 ne suka musulunta a wurin wa’azin kungiyar Jama’atu Izalatul Bid’ah Wa Ikamatis Sunnah na kasa da ta gudanar a garin Miya da ke karamar Hukumar Ganjuwa a ranar Asabar da Lahadin da suka gabata.
A jawabin shugaban Majalisar Malamai ta kasa ta kungiyar Sheikh Sani Yahaya Jingir ya ce za su tallafa da kayan karantarwa da baburan hawa don aikin da’awa a yankunan da mutanen suka musulunta. Kuma ya ja hankalin Musulmi su kasance masu hakuri tare da shirya wa zaben shekarar 2015 ta hanyar jawo kuri’unsu kusa da gudanar da siyasa cikin tausayi da gaskiya.
Kuma ya ja hankalin Gwamnatin Tarayya cewa ta fitar da dukiya a tono albarkatun kasa don a raba mutane da matsalolin da suke fiskanta a wannan lokaci. “Su ma jami’an tsaro su kasance masu juriya su daina tsoron mutanen da suke fitowa don ta’addanci,” inji shi.
Sheikh Jingir ya bayyana matsalar Boko Haram a matsayin wani shiri na karya don cin zarafin mutanen Arewa tare da yi musu lahani kafin zabe mai zuwa.
Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar na Jihar Bauchi, Sheikh Salisu Sulaiman Ningi, ya ce wa’azin ya yi albarka saboda musuluntar mutum 28, don haka sun yi farin ciki burin kungiyar ya cika saboda duk wanda ya musulunta an gafarta masa zunubansa ya koma kamar ranar aka haife shi.
Ya ce a matakin jiha za su yi hobbasa don ganin an karantar da mutanen don haka ya bukaci jama’a su nuna kyakkyawar dabi’a ga wadanda suka musulunta da sauran jama’ar Musulmi don a jawo wadanda ba su musulunta ba su ma su shigo addinin Musulunci.
Ya ce Musulmi shi ne mai umarni da abu mai kyau da hani daga mummuna, saboda haka mai wa’azi dole ya kasance mai hakuri har lokacin da mutane za su karbi kiransa.
Shugaban Majalisar Jihar Bauchi Alhaji Yahaya Mohammed Miya ya yi nasiha ne tare da gode wa kungiyar Izala kan kawo wa’azin mahaifarsa. Ya ja hankalin ’yan siyasa musamman ’yan Arewa kan su kauda ha’inci da cin kafar juna a siyasance, su kuma ’yan siyasar Arewa da masu hannu da shuni su sanya kishi cikin zuciyarsa don ciyar da wannan yanki gaba, su nisanci siyasar zamba da gaba da bata ’ya’yan talakawa, “kowane dan siyasa ya fito da manufofinsa ya bayyana wa jama’a don su zabe shi ta hanyar da ta dace,” inji shi.
Hakimin Miya Alhaji Sulaiman Yakubu ya gode wa kungiyar ne kan zuwa kasarsa don yin wa’azin kasa, inda ya nuna farin ciki game da musuluntar mutum 28. Ya gode wa shugabannin kungiyar da jama’ar da suka halarci wa’azin aka gudanar da shi lafiya ba tare da hayaniya ko tashin hankali ba. Ya ja hankalin Musulmi kan su tsaya da kafafunsu don yin aiki tukuru domin neman shiga Aljanna ranar gobe kiyama.