Mutum 3 sun kamu da Kyandar Biri a Gombe

An yi gargadin cewa cutar takan iya yaduwa daga dabba zuwa mutum.

Mutum 3 sun kamu da Kyandar Biri a Gombe

Gwamnan Jihar Gombe, Inuwa Yahaya

Rahotanni sun tabbatar da cewa cutar kyandar biri ta harbi mutum uku a rukunin gidajen Gwamnatin Tarayya na (Lowcost) da ke Jihar Gombe.

Kwamishinan Lafiya na jihar, Dokta Habu Dahiru ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Yammacin Talatar nan.

Dokta Dahiru ya ce an samu mutane 19 da ake zargin suna dauke da cutar a fadin jihar, wadanda  aka dauki samfurin jininsu kuma gwaji ya tabbatar mutum 3 daga ciki na dauke da ita.

Da yake gargadi kan wannan barazana, Kwamishinan wanda ya ce Jihar Gombe ta shiga sahun jihohin da aka samu bullar cutar, ya kuma bukaci al’ummar jihar da su gaggauta kai rahoton duk wata alama da suke zargin cutar ce ga mahukuntan lafiya mafi kusa.

A cewarsa, Ma’aikatar Lafiya za ta yi duk iya kokarinta na ganin an dakile cutar kafin ta yadu sosai a tsakanin jama’a domin cutar takan iya yaduwa daga dabba zuwa mutane.

Sai dai ya ce kawo yanzu ba a samu asarar rai ba cikin wadanda ake zargin sun kamu da cutar, amma dai ana son jama’a su yi taka-tsan-tsan.

Kwamishinan ya kuma ankarar da jama’a dangane da alamomin cutar da suka hada da zazzabi da ciwon kai da bayyanar manyan kuraje a jikin mutum.