Mutum 3 sun kamu da zazzabin Lassa a Bauchi, ana binciken wasu 12
Hukumar lafiya a matakin farko ta Jihar Bauchi ta tabbatar da cewa mutum uku sun kamu da zazzabin Lassa a jihar sannan ta ce ana zargin wasu 12 sun kamu da cutar. Babban sakataren hukumar a Bauchi Dakta Rilwan Muhammed ne ya bayyana hakan a yau Juma’a ga manema labarai, inda ya ce mutum 15 […]
Hukumar lafiya a matakin farko ta Jihar Bauchi ta tabbatar da cewa mutum uku sun kamu da zazzabin Lassa a jihar sannan ta ce ana zargin wasu 12 sun kamu da cutar.
Babban sakataren hukumar a Bauchi Dakta Rilwan Muhammed ne ya bayyana hakan a yau Juma’a ga manema labarai, inda ya ce mutum 15 ake zqrgi sun kamu kuma an tabbatar da uku daga ciki, yayin da ake ci gaba da tantance jinin sauran 12.
Dakta Rilwan ya ce barkewar cutar ta baya-bayan nan ta shafi kananan hukumomin Toro da Tafawa Balewa da Bauchi da Bogoro da kuma Dass. Ya kuma ce hukumar ta kashe kudi sosai domin bincika kwayar cutar a jihar musamman a Karamar Hukumar Toro, imda abin ya fi kamari.
Rilwan Muhammed ya ce tuni hukumar ta tsara hanyoyin kauce wa mace-mace ta hanyar zuke cutar daga jinin wadanda suka kamu a-kaì-a-kai wato dialysis.
“Mun mika bukatarmu ga gwamna ta sayen imjin yin dialysis ga wadanda cutar ta kama saboda dukkansu suna fama da matsalar koda,” in ji shi. “Sannan kuma mun tanadi jakar jini 10 a babban asibitin Bauchi saboda aikin gaggawa.”
Ya ci gaba da cewa: “Makon da ya gabata gwamnatin tarayya ta ba mu kwayoyin magani da kuma kayan kare kai na ma’aikatan lafiya da ake amfani da su yayin ganowa da kuma kula da masu cutar.”
Ya kuma ce yanzu haka likitoci suna tsoron duba duk wani maras lafiya mai fama da kowane irin zazzabi a jihar Bauchi, abin da ya sa mahukunta suka yi wani zaman shawo kan matsalar.
Sannan ya koka kan dabi’ar wasu matasa a Karamar Hukumar Alkaleri da suke kama beraye kuma suke sayar wa jama’a kan naira 100. Saboda haka ya yi kira ga iyaye da su ja kunnen ‘ya’yansu domin hana cutar ci gaba da yaduwa.