Mutum 3 sun mutu a hasatrin jirgin sojin Nijar
Duka mutum ukun da ke cikin jirgin sun mutu, yayin da gwamnatin kasar ta fara bincike domin gano dalilin aukuwar hatsarin.
Rahotanni daga kasar Nijar na nuni da cewa mutum uku sun mutu a hatsarin da ya rutsa da jirgin saman sojin kasar mai saukar ungulu a ranar Litinin.
Ma’aikatar tsaron kasar ta ce, hatsarin ya auku ne bayan dawowar jirgin daga atisayen horo kamar yadda saba.
- Gobara ta lakume dukiyar N37bn ranar Kirsimeti a Kwara
- Sojoji sun kashe ’yan ta’addan ISWAP 140 a watan Disamba
“Duka mutum ukun da ke cikin jirgin sun mutu, duk da kokarin ceto su da aka yi,” in ji ma’aikatar.
Jirgin, kirar Rasaha Mi-17, ya samu a kasi ne a daidai lokacin da ya yi kokarin sauka a filin jirgin sama na sansanin soji da ke Niamey.
Ma’aikatar ta kara da cewa an fara bincike domin gano silar aukuwar hatsarin.