Mutum 3 sun mutu a rikicin coci a Taraba
Rahotanni, sun nuna cewa rikicin ya samo asali ne sakamakon wata taƙaddama tsakanin mambobin cocin biyu.
Rundunar ’Yan sandan Jihar Taraba, ta tabbatar da mutuwar mutum uku sakamakon rikici da ya faru tsakanin mabiya cocin United Methodist Church in Nigeria (UMCN) da kuma na Global Methodist Church (GMC).
Kakakin rundunar ’yan sandan, SP Usman Abdullahi, ya bayyana cewa rikicin ya faru ne a ranar Lahadi a Ƙaramar Hukumar Karim-Lamido.
- Cin Zarafi: NHRC ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 339 a Gombe a 2024
- Abba ya miƙa sunayen sabbin kwamishinoni ga majalisar dokokin Kano
Rahotanni, sun nuna cewa rikicin ya samo asali ne sakamakon wata taƙaddama tsakanin mambobin cocin biyu.
Rikicin ya sa gwamnatin jihar bayar da umarnin rufe hedikwatar cocin UMCN da ke Jalingo.
Rundunar ta ce an kama mutum shida da ake zargi da hannu a rikicin, sannan an tura jami’an tsaro yankin domin tabbatar da zaman lafiya.
Bincike, ya nuna cewa taƙaddamar ta samo asali ne daga rikicin shugabanci tsakanin UMCN da GMC, wanda ya raba kan mambobin cocin gida biyu, har wasu suka ware tare da kafa nasu tsagin.