Mutum 3 sun mutu yayin ciro waya daga masai a Kano
Mutum na hudu da ya shiga masan ya tsallake rijiya da baya
Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da rasuwar mutane uku a garin ’Yar Gwanda da ke Karamar Hukumar Tsanyawa a jihar a lokacin da suka yi kokarin shiga masai don dauko wata wayar hannu daga ciki.
Kakakin Hukumar ta Kashe Gobara ta Jihar’ Kano Saminu Yusuf Abdullahi ya bayyana cewa tunda farko wayar salular wani magidanci mai suna Danjuma Black dan kimanin shekara 60 ta fada cikin masai inda ya shiga da niyyar dauko ta.
Da aka ji shiru shiru bai fito ba sai dansa mai suna Ibrahim ya shiga da niyyar ceto mahaifinsa, shi ma bai fito ba.
“Hakan ya sa wani mai suna Aminu Key Guy shi ma ya shiga da niyyar ceto su, shi ma dai bai fito ba.
“A nan ne mutum na hudu mai suna Abbas Alhassan ya shiga da niyyar ceto wadancan mutane ukun shi ma dai kamar sauran bai fito ba.
“Daga nan ne aka kira jami’anmu da ke Tsanyawa inda suka zo suka fito da dukkanin mutane hudun.”
Saminu ya kara da cewa “An yi nasarar fito da mutum na karshen da ransa, amma ukun farkon sun fita daga hayyacinsu.”
Saminu Abdullahi ya ce bayan sun fito da mutanen ne suka mika su ga ofishin ’yan sanda na Tsanyawa inda aka kai su asibiti a inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsu.