Mutum 3 sun rasu a arangama tsakanin Sojoji da ‘yan Shi’a

Rundunar sojojin Najeriya ta ce, an kashe mutum uku tare da raunata mutane da dama a arangamar da aka yi tsakanin ‘yan shi’a da sojoji a jiya Litinin a Kugbo dake Abuja. A wata sanarwa da aka fitar a shafin Facebook na cewa, an raunata sojoji hudu a arangamar da aka yi mabiya shi’ar. A […]

Mutum 3 sun rasu a arangama tsakanin Sojoji da ‘yan Shi’a

Rundunar sojojin Najeriya ta ce, an kashe mutum uku tare da raunata mutane da dama a arangamar da aka yi tsakanin ‘yan shi’a da sojoji a jiya Litinin a Kugbo dake Abuja.

A wata sanarwa da aka fitar a shafin Facebook na cewa, an raunata sojoji hudu a arangamar da aka yi mabiya shi’ar.

A jiya Litinin ne da misalin karfe 3 na yamma rikicin ya kaure tsakanin sojojin da mabiya shi’an lokacin da sojojin ke bakin aiki a gadar dake tsakanin Kugbo da Karu da ke wajen Abuja.