Mutum 3 sun shiga hannu kan sace tagogin makaranta a Gombe
Zuwa yanzu, rundunar ta cafke mutum uku da zargi da fasa makarantar.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta cafke wasu mutum uku da ake zargi da fasa makarantar firamare ta Magaba da ke Bajoga, a Ƙaramar Hukumar Funakaye, a Jihar Gombe.
Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce an kama su ne bayan shugaban makarantar, Malam Buba Chiroma, ya kai rahoto ofishin ’yan sanda a ranar Juma’a, 22 ga watan Agusta, 2025.
Chiroma, ya bayyana cewa da misalin ƙarfe 8:20 na safe ne aka gano an fasa tagogin makarantar, amma ba su san waɗanda suka aikata laifin ba.
DSP Abdullahi, ya ce bayan kai rahoton, jami’an tsaro tare da ’yan sa-kai suka je wajen, inda suka cafke mutum uku da ake zargi kuma suka ƙwato wasu tagogi da aka lalata a matsayin shaida.
Ya ƙara da cewa bincike yana gudana, kuma za a sanar da al’umma abin da ake ciki.
Haka kuma, ya yi kira ga jama’a da su taimaka wajen tsaron makarantu musamman a lokacin ake hutu, tare da sanar da ’yan sanda duk wani abu da suke da shakku a kai.