Mutum 3 sun shiga hannu kan yunkurin sace wani a Bauchi

Mutanen sun ci gaba da yi wa mutumin barazana idan bai saka musu kudin da suka nema ba.

Mutum 3 sun shiga hannu kan yunkurin sace wani a Bauchi

Wasu ‘yan sandan Nijeriya

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta kama wasu mutum uku da ake zargi da laifin hada baki da yunkurin garkuwa da mutane a jihar.

Kakakin rundunar, SP Ahmed Wakil ne, ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi a Bauchi.

Ya ce rundunar, a yaki da garkuwa da mutane da sauran munanan laifuka, na ci gaba da samun kyakkyawan sakamako a jihar.

“A ranar 7 ga watan Maris 2024 da misalin karfe 2 na rana, wani mutum daga kauyen Badakoshi a Karamar Hukumar Bauchi, ya shigar da kara a sashen yaki da masu garkuwa da mutane (AKU).

A cewarsa, a ranar 4 ga watan Maris, da misalin karfe 8 na dare, wani mutum ya kira shi ya gabatar da kansa.

“Ya yi masa barazanar sai ya samo masa Naira miliyan biyar.”

Kakakin, ya ce mutumin ya yi barazanar sace shi (Yahaya) ko kuma wani daga iyalinsa.

Bayan kwanaki kadan, wadanda ake zargin sai suka aike wa mutumin lambar asusun wani mai POS domin ya sanya kudin da suka nema, in ji Wakil.

“Mutanen sun barazanar cewar sun san komai nasa da dukiyarsa da iyalansa, inda suka ce komai nasa zai kasance cikin hatsari.”

A cewarsa, bayan samun bayanan sirrin, Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Auwal Musa, ya umarci sashen binciken manyan laifuka (CID) da su binciki lamarin cikin nutsuwa.

“An gudanar da binciken ne ta hanyar amfani da fasahar zamani, inda aka kamo su a garin Birnin Kudu na Jihar Jigawa.

“An kama wadanda ake zargin ne daban-daban a garin Birnin Kudu da ke Jihar Jigawa da kuma Kaltunga ta Jihar Filato,” in ji shi.

Kakakin ya bayan gudanar da bincike wadanda ake zargin sun amsa laifin da ake zargin su da shi.

Ya ce za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike a kan su.

Dole talauci ya yi katutu a Arewa!

Hauhawar farashin kayayyaki ta ƙaru da kaso 33 a Najeriya — NBS

Kotun Ƙoli ta yi watsi da buƙatar rushe Hukumar EFCC

HOTUNA: Jana’izar tsohon Babban Hafsan Sojin Ƙasa Lagbaja