Mutum 30 sun rasu a harin bam na Maiduguri

Akalla mutum 30 ne suka rasu sannan da dama suka samu raunuka sakamakon fashewar bam a wata mota a kusa da kasuwar Jagwal da ke Maiduguri babban birnin Jihar Borno a ranar Talatar da a gabata.Wannan shi ne hari mafi muni ga birnin na Maiduguri tun watan Maris din da ya gabata, kuma sojoji sun […]

Mutum 30 sun rasu a harin bam na Maiduguri

PIC.15. A SCENE OF BOMB BLAST AT THE POST OFFICE AREA OF MAIDUGURI IN BORNO ON TUESDAY (14/1/14). 258/14/1/14/ABI/NAN

Akalla mutum 30 ne suka rasu sannan da dama suka samu raunuka sakamakon fashewar bam a wata mota a kusa da kasuwar Jagwal da ke Maiduguri babban birnin Jihar Borno a ranar Talatar da a gabata.
Wannan shi ne hari mafi muni ga birnin na Maiduguri tun watan Maris din da ya gabata, kuma sojoji sun dora alhakin harin kan mayakan kungiyar Boko Haram.
Mazauna birnin da wasu majiyoyin asibiti a Maiduguri sun tabbatar da cewa mutum 30 aka kashe, kuma akwai yiwuwar adadin ya fi haka, sai dai ’yan sanda sun ce mutum 17 ne suka rasu, sai dai suna ci gaba da binciko wadanda suka mutu.
Shaidu sun ce fiye da motoci 20 da Keke NAPEP biyar suka kone kurmus daga wutar da ta tashi daga motar da ake zargin bam din ya tashi. Wutar ta kuma cinye rumfuna da shagunan da galibinsu na matasa ne da ke sayar da katunan waya da sauran kayayyakinsu.
Wakilanmu sun samu bayanin cewa masallatta da dama da suke Sallar Azahar a wani masallaci da ke kusa da wasu da ke zaune a gefe suna alwala sun mutu.
Wani dan sanda mai kula da zirga-zirgar abubuwan hawa da mata masu sayar da kosai da masu motoci da dama da wani fitaccen mai sayar da tsire Malam Amadu Faragai da ’yan aikinsa hudu, wadanda duka suke kusa da kasuwar wayoyin hannu da ake kira GSM billage sun rasu a harin.
A wurin da bam din ya tashi ya yi wani wawakeken rami da zai iya cinye babur, yayin da sassan jikin dan Adam da sauran kayayyaki da sassan motoci suke barbaje ko’ina.
Mutane da dama da harin ya halaka sun yi daga-daga ta yadda ba a iya gane su, inda wani mai suna Salisu Bala Mai Memory da ke sayar da katin waya a kasuwar wanda ya tsallake rijiya da baya a harin ya ce, “Harin ya ci kanena, kuma na iya gane shi ne kawai ta takalmarsa, amma naman jikinsa ya yi daga-daga.”
Mazauna birnin da dama sun ce sun ji karar fashewar bam din daga nisan kilomita hudu.
Rundunar sojojin Najeriya ta ce zargin mayakan Boko Haram da ta da bam din, kamar yadda ta fada cikin wata sanarwa dauke da sanya hannun Kakakin Runduna ta Bakwai Kanar Mohammed Dole.
Gwamnan Jihar Borno Kashim Shettima wanda ya yi Allah wadai da harin ya bukaci a gudanar da cikakken bincike a kai.
Kakakin Gwamna Isa Umar Gusau ya ce Gwamnan ya la’anci harin tare da umartar jami’an tsaro su gudanar da cikakken bincike kan tashin bam din wanda ya haifar da tarzomar matasa da suka shiga kone-kone da karya doka da oda, inda ya nanata kudirin gwamnatinsa na ci gaba da kare rayuka da dukiyar jama’ar jihar.
A yayin tarzomar matasan da ke zargin harin na da alaka da siyasa, sun kone ofishin kamfe na tsohon Gwamnan Jihar Sanata Ali Modu Shariff da ke kusa da UTC, yayin da wasu suka nufi gidansa da ke hanyar barikin soja da gidan mahaifinsa da ke hanyar Damboa kafin sojoji da ’yan sanda su tarwatsa su. Kuma an kone gidaje da motocin da suke dauke da fosta-fostan tsohon Gwamnan a yayin tarzomar.