Mutum 3,000,000 sun nemi aikin N-Power a mako guda
Mutum miliyan uku ne suka cike neman gurbin aikin matasa dubu dari hudu na N-Power a cikin mako daya da aka bude yin rijistar shirin. Ma’aikatar Agaji da Kyautata Rayuwar Al’umma ta ce zuwa ranar Juma’a 3 ga watan Yuli, mutum miliyan uku sun yi rijistar neman aikin N-Power, daga ranar Juma’ar 26 ga watan […]
Mutum miliyan uku ne suka cike neman gurbin aikin matasa dubu dari hudu na N-Power a cikin mako daya da aka bude yin rijistar shirin.
Ma’aikatar Agaji da Kyautata Rayuwar Al’umma ta ce zuwa ranar Juma’a 3 ga watan Yuli, mutum miliyan uku sun yi rijistar neman aikin N-Power, daga ranar Juma’ar 26 ga watan Yuni da aka kaddamar da shirin a karo na uku.
- N-Power: An kama mai damfarar ‘yan gudun hijira
- N-power: Abun da ya kamata ku sani kafin fara rijista
“Nan gaba kadan za a rufe shafin neman gurbin aikin domin a tantance matasan da za su amfana”, inji Mai Taimaka wa Darektan Yada Labarai na Ma’aikatar, Rhoda Iliya.
Karo na uku ke nan da mutanen ke neman aikin na N-Power suke yin rijista ta intanet yayin da matasan rukunin farko da na biyu ke bankwana da shirin.
A baya ministar ma’aikatar, Sadiya Umar Faruk ta sanar cewa ana shirin kawo karshen aikin wadanda suka amfana da shirin a rukunin farko da na biyu, inda ta nemi masana’antu masu zaman kansu su samar musu aiki.