Mutum 32 sun mutu a hatsarin kwale-kwale a Zamfara

Shehu Aminu Gummi ya ce fasinjoji kadan ne aka ceto, yayin da sauran suka bace a kogin.

Mutum 32 sun mutu a hatsarin kwale-kwale a Zamfara

Akalla mutum 32 ciki har da mata da kananan yara sun mutu sanadiyyar hatsarin wasu kwale-kwale biyu da su ka yi karo da juna a cikin gulbin garin Gummi a Mashayar ’Yan Tauri da ke Jihar Zamfara.

Lamarin a cewar wani mazaunin Gummi, Safiyanu Dan Iya, ya faru ne a lokacin da wani jirgin ruwa dauke da fasinjoji sama da 40, yawancinsu manoma, da ke kan hanyar zuwa gonakinsu, ya fara tangal-tangal a cikin ruwan sakamakon matsanancin lodin da aka yi masa.

Hakan ya sa direban wani kwale kwale ya yi yunkurin ba su agaji sai su ka yi taho mu gama da juna, inda duka jiragen biyu suka nutse a cikin ruwan.

Wani mazaunin garin Shehu Aminu Gummi ya ce fasinjoji kadan ne aka ceto, yayin da sauran suka bace a kogin.

“Bayan da kwale-kwalen ya kife kuma ya nutse a cikin kogin, an dauki kusan sa’o’i biyu kafin wadanda suka tsira da rayukansu su bayyana a saman ruwan.

“Jirgin ruwan ya kife da misalin karfe 10 na safe kuma wadanda suka tsira sun bayyana a saman ruwan da misalin karfe 12 na rana.

“Duk da cewa an ci gaba da aikin ceto har zuwa karfe 8 na dare, babu wani karin mutum a cikin wadanda abin ya shafa da aka samu a mace ko a raye.”

Shi ma da yake nasa jawabin, Sarkin Fadar Gummi, Alhaji Mahmud S. Fada, ya tabbatar da cewa an ceto mutane takwas “amma banda su, ba mu sake ganin kowa ba.

Aminiya ta ruwaito cewa lamarin shi ne na biyu da ya faru a yankin, inda shekaru biyar da suka gabata wani kwale-kwale dauke da fasinjoji ya kife a wannan gulbin, sai dai a wancan karon ba a samu asarar rai ba.

Batun kifewar kwale-kwale dai ba sabon abu ba ne a Nijeriya, inda a lokuta da dama hatsarin ke zuwa da muni sakamakon irin ƙazamin lodin da ake yi wa jiragen ruwan.

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja