Mutum 3,200 sun amfana da zakkar miliyan N10 a Kazaure
Masarautar Kazaure ta ce an rana zakkar ce ga mabukata a tsakanin gundumomi tara a yankin
Masarautar Kazaure a Jihar Jigawa ta raba zakkar kudi ta Naira miliyan 10 ga marasa galihu 3,200 a yankin.
Mai magana da yawun masarautar, Malam Gambo Garba ne ya bayyana haka a tattaunawarsu da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ranar Juma’a a Dutse, babban birnin jihar.
- Ganduje ya yi gargadi kan yakin zabe a wuraren ibada
- Jirgin kasan Abuja-Kaduna zai dawo ranar Litinin
Malamin ya ce an rabar da kudin ne ga wadanda suka cancanta a gundumomi tara da ke masarautar.
A cewar Garba, Shugaban Kwamitin Tara Zakka na Masarautar, Alhaji Bala Muhammad, ya ce, nan ba da dadewa ba za a fadada raba zakkar da aka tara zuwa ga majinyatan da ke asibitoci daban-daban a yankin Kazaure.
Garba ya kara da cewa, Sarkin Kazaure, Alhaji Najib Hussaini, ya ba da tabbacin masarautar za ta ci gaba da ba da himma wajen karba da kuma raba Zakkar kamar yadda addini ya tanadar.
(NAN)