Mutum 36 sun mutu a hadarin jirgin kasa a Girka
Ministan Sufurin kasar, Kostas Karamanlis ya yi murabus.
Akalla mutane 36 suka mutu yayin da wasu 85 suka jikkata a wani hadarin jiragen kasa da ya faru a birnin Larissa na Girka.
Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya ruwaito cewa, lamarin ya auku ne da tsakar daren jiya Talata, ko da ya ke da dama daga cikin fasinjojin sun samu tsira da rayukansu.
Rahotanni sun bayyana cewa jiragen biyu sun yi taho mu gama ne da tsakar dare jiya Talata yayin da suka ritsa da wata mota ta daban da ke kan hanya wadda ta kone kurmus dauke da fasinja.
Masu aikin ceto sun yi nasarar kai wa yankin da hadarin ya faru sa’o’i kusan 5 bayan faruwarsa, inda suka iya nasarar zakulo masu sauran numfashi a ciki.
Tuni jami’an tsaro suka kame daraktan tashar jirgin kasan, wani dattijo mai shekaru 59 wanda aka alakanta hadarin da kuskuren shi.
Bayanai sun ce ko wanne lokaci daga yanzu ne za a sanar da hukuncin da za a yi wa dattijon wanda ke kula da aikin bayar da hannu a tashar jiragen kasan wadda ke da alhakin kulawa da layukan dogon da hadarin ya faru.
Tuni dai Ministan Sufurin na Girka, Kostas Karamanlis ya yi murabus bayan ya kai ziyara wurin da wannan ibtila’in ya auku.